1448AH: Tinubu ya Taya Musulmi Murna, Ya Tabo Hijirar Annabi SAW daga Makkah zuwa Madina

1448AH: Tinubu ya Taya Musulmi Murna, Ya Tabo Hijirar Annabi SAW daga Makkah zuwa Madina

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya daukacin al'ummar Musulmi a Najeriya murnar shiga sabuwar shekarar Hijira ta 1448AH
  • Mai girma shugaban kasar ya bukaci Musulmi da sauran ’yan Najeriya su rungumi kishin kasa da kyawawan dabi’u
  • Ya ce darussan Hijira sun hada da sadaukarwa, hakuri da dogaro ga Allah, kana ya yi addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa da ci gaba ga Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmi a Najeriya da ma duniya baki daya murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.

Hakan na zuwa bayan kalandar musulunci ta shiga sabuwar shekara a yau Talata, 16 ga watan Yuni, 2026 wanda ya kama 1 ga watan Muharram 1448 bayan Hijira.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taro a Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya taya musulmi murna

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi martani da Janar Rabe Abubakar ya mutu a hannun 'yan bindiga

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ya kuma yi amfani da wannan dama wajen kira ga Musulmi da daukacin ’yan Najeriya da su kara rungumar kishin kasa da kyawawan dabi’un zama nagartattun ’yan kasa.

Sakon taya murnar mai girma Tinubu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar yau Talata a Abuja.

Tinubu ya ce sabuwar shekarar Hijira a addinin musulunci tana tunatar da Musulmi muhimmancin Hijirar da fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) ya yi daga Makka zuwa Madina.

Tinubu ya tuna hijirar Annabi SAW

A cewarsa, darussan da ke cikin Hijirar sun hada da sadaukarwa, sabuntawa, hakuri da kuma cikakken dogaro ga tsarin Allah Madaukakin Sarki.

“Yayin da Musulmi suka shiga sabuwar shekarar Hijira, shugaban kasa yana fatan za su su yi koyi da kyawawan darussan Hijira daga Makka zuwa Madina, wadda ta zama farkon kalandar Musulunci,” in ji sanarwar.

Shugaba Tinubu ya bukaci Musulmi da sauran ’yan Najeriya gaba daya da su sake jajircewa wajen zama nagartattun ’yan kasa masu kishin ci gaba.

Ya ce ayyukan alheri, hakuri da juna, gaskiya da rikon amana wajen aiki na da matukar muhimmanci wajen karfafa hadin kai, tsaro da ci gaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira tiriliyan 5 kan tsaro, za a dauki sababbin ƴan sanda 50000

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da wasu jiga-jigan gwamnati a babban masallaci na kasa da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Addu’ar zaman lafiya da arziki

Shugaban kasar ya yi addu’ar Allah Ya sanya sabuwar shekarar Hijira ta zo da albarka, zaman lafiya da wadata ga gidajen al’ummar Najeriya.

Ya kuma roki Allah Ya ci gaba da shiryar da Najeriya zuwa tafarkin ci gaba, hadin kai da nasara, kamr yadda tashar Channels tv ta kawo.

An shiga sabuwar shekara a musulunci

A wani labarin na daban, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 a Najeriya bayan ganin wata a yammacin ranar Litinin, 25 ga watan Yuni, 2026.

Sanarwar da fadar Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar III ta fitar ta nuna cewa ranar Talata, 16 ga Yunin 2026 ne ta kasance 1 ga watan Muharram na shekarar 1448.

Sarkin Musulmin ya taya Musulmi a faɗin Najeriya da duniya murnar sabuwar shekarar Musulunci, sannan ya buƙace su da su yi amfani da wannan lokaci wajen addu’a da ƙara ƙaimi wajen bin dokokin Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262