Dubun wani likitan bogi ta cika bayan shekaru 11 yana duba marasa lafiya a Kaduna

Dubun wani likitan bogi ta cika bayan shekaru 11 yana duba marasa lafiya a Kaduna

Ma’aikatar sharia ta gwamnatin jahar Kaduna ta gurfanar da wani likitan bogi mai suna Sa’idu Ahmed a gaban kotun majistri a kan tuhumarsa da take yi da yin sojan gona tare da kirkirar da amfani da takardun karatu na bogi.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar sharia’ar ta fitar, wanda ke dauke da sa hannun kwamishiniyar sharia ta jahar Kaduna, Aisha Dikko, ta bayyana cewa a yanzu haka kotun ta bada umarnin garkame Saidu a gidan gyara hali zuwa ranar 16 ga watan Maris.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Kaduna ta kalubalanci hukuncin kotu na sakin yan shia 92

Daily Nigerian ta ruwaito sanar ta kara da cewa Saidu ya kwashe sama da shekaru 11 yana aiki da ma’aikatar kiwon lafiya ta jahar Kaduna a matsayin likita, biyo bayan samun takardar koke a kansa ne gwamnan jahar Kaduna ya bada umarni ga ma’aikatar ta bincike shi.

Ma’aikatar ta kafa kwamitin mutane hudu domin ta bincike lamarin yadda ya kamata ta hanyar bincikar sahihancin takardun kammala karatun likitanci da Saidu yake amfani dasu tare da makarantun da ya yi ikirarin halarta, sai kuma su binciki ko yana da rajist da kungiyar likitocin Najeriya.

Sakamakon binciken kwamitin ya tabbatar da Saidu ya shirya takardun bogi ne kuma ya yi amfani dasu wajen samun aiki da gwamnatin jahar Kaduna har ya kwashe tsawon shekarun nan.

“Bayanai daga jami’ar ABU da hukumar likitoci Najeriya sun bayyana Saidu bai taba samun gurbin karatu a jami’ar ABU ba, kuma bai kammala karatu a ABU ba, sa’annan ba shi da rajista da hukumar likitocin Najeriya, MDCN.” Inji shi.

Sai dai koda aka karanta masa tuhume tuhumensa, sai Saidu ya musantasu, sa’annan ya nemi kotu ta bada belinsa, amma daraktan shigar da kara na jahar Kaduna ya nemi kotu ta yi fatali da bukatar Saidu na samun beli, sa’annan ya nemi karin lokaci domin kammala bincike a kan Saidu.

Bayan sauraron bangarorin biyu, Alkalin kotun ya dage shariar zuwa ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2020.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel