Rusau: El-Rufa'i ya bawa 'yan 'kasuwar bacci' wa'adin kwana uku

Rusau: El-Rufa'i ya bawa 'yan 'kasuwar bacci' wa'adin kwana uku

Gwamnatin jihar Kaduna ta ba wa ‘yan Kasuwar Barci da ke Tudun Wada a Kaduna wa’adin kwanaki uku.

An manna sanarwan ne a shagunan da ke kasuwar a safiyar Asabar kuma an umarci ‘yan kasuwar dasu bar kasuwar zuwa ranar Litinin.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Haruna Dabai, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa hankulan ‘yan kasuwar ya matukar tashi.

“Mun zo kasuwar da safiyar Asabar inda muka samu sanarwar an manna a shagunanmu. An bamu kwanaki uku a kan mu tashi. Mun yi magana da lauyanmu amma kamar yadda kuke gani, lamarin ya faru ne a ranakun karshen mako.

Rusau: El-Rufa'i ya bawa 'yan 'kasuwar bacci' wa'adin kwana uku

Rusau: El-Rufa'i ya bawa 'yan 'kasuwar bacci' wa'adin kwana uku
Source: UGC

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi II: Al'ummar unguwar Ja'en sun nesanta kansu daga takardar korafi, zasu yi karar majalisa

“Muna kira ga ‘yan kasuwar da su kwantar da hankulansu don muna kokarin ganin yadda zamu shawo kan matsalar cikin lumana,” yace.

Jaridar Daily Trust ta ga takardar wacce daraktan KASUPDA, Isma’il Umar-Dikko yasa hannu da kwanan wata 6 ga watan Maris.

Babban daraktan ya ce hakan ya zama dole, idan aka yi duba da yadda gwamnatin jihar Kaduna ta dage wajen aiyukan gyaran kasuwannin jihar.

“Rashin biyayya ga wannan umarnin zai jawo hukumar ta rushe shagon duk yadda ta same shi, kamar yadda sashi na 60 na dokokin KASUPDA na 2018 ya tanadar.” Takardar ta ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel