Miyagu sun tare hanyar Kaduna, sun sace mutane da dama, sun kashe na kashewa

Miyagu sun tare hanyar Kaduna, sun sace mutane da dama, sun kashe na kashewa

Gungun miyagu yan bindiga sun tare babbar hanyar Birnin Gwari zuwa cikin garin Kaduna inda suka bude ma matafiya wuta, suka kashe na kashewa, suka sace na sacea sa’annan suka raunata wasu da dama.

Jaridar Premium Times ta ruwaito yan bindigan sun kai hare haren ne da yammacin ranakun Asabar da Lahadi na makon da ya gabata, inda ta dace daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu akwai dalibai da suka zana jarabawar JAMB a Kaduna, suna hanyarsa ta komawa gida a Birnin Gwari.

KU KARANTA: Mutane 15 sun mutu, gine gine 50 sun rushe a fashewar bututun mai a Legas

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa akwai wani mutumi mai suna Ibrahim Idris da yan bindigan suka kashe, wanda direban tsohon dan majalisar tarayya ne, Alhaji Adamu Shekarau.

Malam Ibrahim ya shiga mota daya ne tare da daliban da yan bindigan suka yi garkuwa da shi, sai kuma wata karamar yarinya da ita ma suka yi awon gaba da ita, duk a cikin motar, a ranar Asabar.

Yan bindigan sun sake komawa kan titin a ranar Lahadi, inda suka sake kashe mutane uku da misalin karfe 4 na rana, sa’annan suka tattara wasu mutane da ba’a tabbatar da adadinsu ba zuwa cikin daji.

Sai dai ko da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kaduna don jin ta bakinsa, Muhammad Jalige, sai yace: “Eh muna da labarin harin da aka kai a ranar Asabar inda aka kashe direban wata mota, amma har yanzu muna jiran samun cikakken rahoton adadin mutanen da aka sace.”

A wani labari kuma, akalla dakarun rundunar Sojojin Najeriya guda 6 ne suka gamu da ajalinsu a sakamakon wani mummunan harin kwantan bauna da mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suma kaddamar a ranar Lahadi a jahar Borno.

Mayakan ta’addancin sun kai ma Sojojin harin ne yayin da suka bude ma ayarin motocin Sojojin wuta a kusa da kauyen Mayanti dake kusa da iyakar Najeriya da kasar Kamaru, yankin da yan ta’adda suka mamaye.

“Mun yi asarar Sojoji guda 6 a wannan harin kwantan bauna da Boko Haram ta kai mana.” Kamar yadda wani jami’in rundunar Soja ya tabbatar ma majiyar Legit.ng.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel