Rashin Tsaro Ya Yi Ƙamari: Yan Sanda Sun Dauki Mataki a Makarantun Katsina
- 'Yan sanda sun ce Sufeto Janar na Najeriya, Olatunji Disu, ya umarci rundunar Katsina ta ƙara tsaurara matakan tsaro a Katsina
- Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da Kuɗi da Gudanarwa, Sulaiman Abdul, ya isar da umarnin yayin rangadin aiki na kwanaki biyu
- Jami’an sun duba katanga, wuraren shiga da fita, guraben tsaro da kuma tattaunawa da shugabannin makarantu kan matsalolin tsaro da hanyoyin magance su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Olatunji Disu, ya umarci tsaurara tsaro a makarantun Katsina.
Disu ya umarci rundunar ‘yan sanda ta Katsina da ta ƙara ƙarfafa tsaro a makarantu da cibiyoyin ilimi a faɗin jihar.

Source: Twitter
Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da Sashen Kuɗi da Gudanarwa, Sulaiman Abdul, ne ya isar da saƙon daga Sufeto Janar yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Katsina, cewar The Nation.
An bukaci tsaurara tsaro a makarantun Katsina
A yayin ziyarar, jami’in ya tantance tsarin tsaro na wasu zaɓaɓɓun makarantu tare da umartar rundunar ta ƙara sintiri da daidaita ayyukan tsaro domin kare makarantu.
Ya ce an umurci rundunar da ta ƙara sintiri, ta inganta tattara bayanan sirri, sannan ta tabbatar da yawan bayyanar jami’an tsaro a kusa da makarantu.
A cewarsa, matakan za su taimaka wajen hana aikata laifukan tashin hankali tare da samar da yanayi mai aminci ga koyarwa da koyo.
Ya ce:
“An umarci rundunar da ta ƙara ƙaimi wajen sintiri, ta ƙarfafa tattara bayanan sirri, sannan ta ci gaba da kasancewa a fili da yawan bayyanar jami’an tsaro a kusa da cibiyoyin ilimi domin hana laifukan tashin hankali da tabbatar da yanayi mai aminci na koyarwa da koyo.”

Source: Facebook
Makarantun da ƴan sanda suka ziyarta
A lokacin rangadin, DIG ɗin ya ziyarci Makarantar ‘Ya’yan ‘Yan Sanda da kuma kwalejin fasaha ta mata da ke ƙaramar hukumar Charanchi, cewar Daily Post.
Ya duba katangar makarantu, wuraren shiga da fita, wuraren zaman jami’an tsaro da kuma yadda aka tura jami’an domin tantance matakan kariyar da ake da su.
Har ila yau, ya gudanar da ganawa daban-daban da shugabannin makarantun domin samun bayanai kai tsaye kan ƙalubalen tsaro da suke fuskanta.
Ya kuma buƙaci shugabannin makarantu su tabbatar da tsauraran matakan kula da shiga makaranta tare da gaggauta sanar da hukumomin tsaro duk wani abin da ya haifar da zargi.
Rahotanni sun ruwaito cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa tsaro a makarantu da kare rayukan ɗalibai da malamai.
'Yan bindiga sun kashe dan kasuwa a Katsina
Mun ba ku labarin cewa 'yan bindiga sun kashe fitaccen ɗan kasuwa kuma manomi, Alhaji Bala Sanin Kawo, bayan sun yi garkuwa da shi a jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa domin kubutar da shi kafin daga bisani a gano gawarsa.
Marigayin ya kasance sanannen manomi kuma ɗan kasuwa a karamar hukumar Dandume da maƙwabtan yankuna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

