Zamfara: Sojoji sun kama masau garkuwa da mutane da motarsu ta daukan makamai

Zamfara: Sojoji sun kama masau garkuwa da mutane da motarsu ta daukan makamai

Dakarun rundunar sojin Najeriya sun samu nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara.

Masu garkuwa da mutanen, wadanda suka boye manyan bindigu kirar AK47 guda uku da alburusai masu yawa a cikin wata mota kirar Volkswagen, sun shiga hannu ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Alhamis.

Masu garkuwa da mutanen biyu da dakarun sojin suka kama sune; Bala Yunusa (wanda aka fi sani da Katako), dan asalin jihar Kaduna mai shekaru 35 da Idris Iliyasu (wanda aka fi sani da Dan Ikara), mai shekaru 37, dan asalin karamar hukumar Ikara da ke jihar Kaduna.

Kakakin rundunar soji na kasa, Sagir Musa, bai bayar da karin bayani a kan lamarin ba bayan manema labarai sun tuntube shi, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Zamfara: Sojoji sun kama masau garkuwa da mutane da motarsu ta daukan makamai
Sojoji
Asali: Depositphotos

Sai dai, wata majiya ta bayyana cewa dakarun rundunar soji sun cafke masu laifin ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Mada daga kauyen Mariri da ke karkashin karamar hukumar Lere a jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: Tura ta kai bango: 'Yan agaji sun kashe 'yan bindiga 17 a Katsina, fararen hula 4 sun mutu

Majiyar ta bayyana cewa masu laifin sun bayyana cewa sunan shugabansu Kachalla Dogo Hamza kuma yana zaune ne a jihar Zamfara.

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa ta fahimci dakarun soji na cigaba da farautar sauran mambobin kungiyar masu laifin domin kama su tare da sauran makamansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel