Yadda Janar Abdulsalami Ya Hana Obasanjo Kai Gwamnatin Tarayya Kotu

Yadda Janar Abdulsalami Ya Hana Obasanjo Kai Gwamnatin Tarayya Kotu

  • Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana yadda ya shawarci Olusegun Obasanjo game da tsayawa takara a zaben 1999
  • Tsohon shugaban mulkin sojan ya ce gwamnatinsa ba ta goyi bayan Obasanjo ba, duk da rade-radin cewa sun taimaka masa ya zama shugaban kasa
  • Abdulsalami ya bayyana cewa ya sassauta ka'idojin rajistar jam'iyyu domin AD ta samu shiga, ta tabbatar da adalci da zaman lafiya a kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya ce ya shawarci Olusegun Obasanjo kan takara a 1999.

Abdulsalami ya bayyana cewa bayan sakin Obasanjo daga gidan yari a 1998, ya ba shi shawarar ya hakura da kudirin tsayawa takarar shugaban kasa.

Shawarar da Abdulsalami ya ba Obasanjo kan takara a 1999
Tsofaffin shugabannin Najeriya a mulkin soja, Abdulsalami Abubakar da Olusegun Obasanjo. Hoto: AbdulsalamiAbaubakar/OlusegunObasanjo.
Source: Twitter

Wadannan bayanai suna kunshe ne a babi na 22 na littafin tarihin rayuwarsa mai suna "Call of Duty," wanda ke dauke da babuka 27 a shafuka 264, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Jarumin fim ya maka INEC, hadimin Wike a kotu, ya buƙaci diyyar N10bn

1999: Abin da Abdulsalami ya fada wa Obasanjo

Ya ce ya gaya wa Obasanjo kai tsaye cewa ya koma gida ya gode wa Allah da yake raye bayan wahalhalun da ya sha, sannan ya manta da batun neman shugabancin kasa.

Abdulsalami ya kuma bayyana cewa a ganawar tasu, ya hana Obasanjo kai Gwamnatin tarayya kotu kan daurin da aka yi masa ba bisa ka'ida ba.

Ya ce ya gargade shi cewa ba a san tsawon lokacin da shari'a za ta dauka ba, yana mai ba da shawarar gwamnati ta duba yiwuwar ba shi diyya.

Abubuwa 2 da Obasanjo ya shirya yi

Abdulsalami ya ce Obasanjo ya zo wajensa bayan fitowarsa daga gidan yari da batutuwa guda biyu masu muhimmanci.

Na farko shi ne kudirinsa na gurfanar da gwamnati a kotu, sannan na biyu gayyatar da jam'iyyar PDP ta yi masa domin neman shugabancin kasa.

Ya ce ya shawarce shi kada ya kai gwamnati kotu saboda hakan ba zai amfani makomarsa ba kuma ba a san lokacin hukunci ba.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalami ya yi zargin akwai lauje cikin nadi kan mutuwar Sani Abacha

Ya kara da cewa ya yi kokarin karkatar da hankalin Obasanjo daga batun shari'ar, kuma tsohon shugaban ya amince da wannan shawara.

Abdulsalami ya magantu kan siyasar 1999 da Obasanjo
Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Abdulsalam Abubakar. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Shawarar da Abdulsalami ya ba Obasanjo

Game da gayyatar PDP, Abdulsalami ya ce ya bukaci Obasanjo ya hakura da takarar shugaban kasa saboda wahalar da ya sha a tsawon shekaru hudu.

Ya ce Obasanjo ya yi dogon numfashi tare da bayyana cewa zai yi tunani a kai kafin ya dawo da amsa, kamar yadda TheCable ya ce.

Sai dai Abdulsalami Abubakar ya ce Obasanjo bai sake tuntubarsa ba bayan wannan tattaunawa, yana mai cewa zai iya tabbatar da hakan da kansa.

Ya jaddada cewa nasarar da Obasanjo ya samu a zaben 1999 ba hujja ba ce da ke nuna gwamnatinsa ta mara masa baya.

A cewarsa, gwamnatinsa ba ta amince da takarar Obasanjo ba, kuma ba ta yi masa aiki domin samun nasara ba.

Abdulsalami ya magantu kan mutuwar Abiola

Mun ba ku labarin cewa Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya kawo wasu karin bayanai game da mutuwar MKO Abiola a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Kokarin da Janar Abdulsalam Abubakar ya yi kan Abiola kafin rasuwarsa'

Abdulsalam ya ce ba a ba tawagar Amurka damar ganin Abiola ba da farko, amma ya ba da umarnin a kai su wajensa.

Ya bayyana cewa Abiola ya fara tari da zufa yayin ganawa da tawagar kafin daga bisani ya rasu, lamarin da ya girgiza kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.