Zargin Rashawa: An Samu Matsala a Shari'ar Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai
- Babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta dage shari’ar Nasir El-Rufai zuwa ranar 24 ga Yunin 2026 saboda rashin halartar wasu da ake kara
- Hukumar ICPC na zargin tsohon gwamnan da almundahana da rashin bin ka’ida wajen gudanar da wasu ayyukan gwamnati a Kaduna
- El-Rufai ya musanta dukkan zarge-zargen tare da cewa gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka bisa tanadin doka da ka’idojin saye da kwangila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kaduna - Babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta dage sauraron shari’ar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bayan wasu mutane biyu da ake kara tare da shi sun gaza bayyana a gaban kotu.
An gudanar da zaman kotun ne ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, 2026, karkashin jagorancin Mai shari’a Rilwanu Aikawa.

Source: Twitter
An samu matsala a shari'ar Nasir El-Rufai
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa cewa El-Rufai ya isa kotun da misalin karfe 9:30 na safe tare da rakiyar jami’an hukumar ICPC da kuma jami’an DSS da ‘yan sanda.
Sai dai zaman kotun bai yiwu kamar yadda aka tsara ba saboda rashin halartar sauran wadanda ake kara tare da tsohon gwamnan.
Daga bisani mai shari’a ya dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Yunin 2026 domin ci gaba da shari’ar.
ICPC na zargin El-Rufai da almundahana
Hukumar ICPC ce ta shigar da karar kan zargin cin zarafin ofis, almundahana da kuma rashin gaskiya wajen tafiyar da kudaden gwamnati, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.
A cewar masu gabatar da kara, an fitar da kudade domin wasu ayyukan gwamnati da ake zargin ba a aiwatar da su yadda ya kamata ba a lokacin mulkin El-Rufai daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Hukumar ta kuma yi zargin cewa an yi watsi da wasu ayyuka ko kuma an gudanar da su ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba.
Masu gabatar da karar sun ce akwai wasu jami’an gwamnatin Kaduna ta lokacin da ake zargin sun shiga harkokin da suka janyo asarar kudade ga gwamnatin jihar.
El-Rufai ya musanta zarge-zargen
Sai dai, The Nation ta rahoto cewa tsohon gwamnan da sauran wadanda ake kara tare da shi sun musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu.

Source: Facebook
El-Rufai ya dage cewa gwamnatinsa ta bi tanadin doka da kuma tsarin gudanar da saye da bayar da kwangila a kan dukkan ayyuka da kwangilolin da ta aiwatar.
A zaman kotun da suka gabata, an saurari muhawara kan sharuddan beli da kuma wasu bukatun farko da lauyoyin masu kare wadanda ake kara suka gabatar.
Rahotanni sun nuna cewa, an tsara cewa zaman ranar Litinin zai karkata ne kan wasu bukatu kafin daga bisani aka sanar da dage karar.
Nasir El-Rufai na tsare tun ranar 16 ga watan Fabrairu bayan dawowarsa daga birnin Alkahira na kasar Masar.
El-Rufai ya mika bukatu ga ICPC
A wani labari, mun ruwaito cewa, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, tare da iyalansa, sun mika bukatunsu ga hukumar yaki da cin hanci ta ICPC.

Kara karanta wannan
Dan majalisar Amurka mai sukar Najeriya ya jinjina wa Tinubu kan dokar ƴan sandan jihohi
El-Rufai da iyalansa sun buƙaci diyyar N15.6bn daga ICPC shugabanta, da sauran jami’anta, sakamakon kama shi, tsare shi, da kuma bayanan ƙarya da aka fitar a kansa.
Wannan buƙata ta biyo bayan iƙirarin da hukumar ta yi na cewa an gano “na’urorin saurarar maganganun mutane ta waya” a gidan El-Rufai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

