Yadda aka yi na zama sabon kaakakin majalisar dokokin jahar Kaduna – Zailani

Yadda aka yi na zama sabon kaakakin majalisar dokokin jahar Kaduna – Zailani

Sabon kakakin majalisar dokokin jahar Kaduna, Yusuf Tanimu Zailani ya bayyana yadda aka yi har ya dare wannan mukami bayan tsohon kaakakin majalisar, Aminu Abdullahi Shagali ya yi murabus a ranar Talata.

Shagali ya mika ma akawun majalisar dokokin jahar Kaduna Alhaji Bello Zubairu takardarsa ta murabus ne da sanyin safiyar Talata, 25 ga watan Feburairu inda ya bayyana a cikin wasikar cewa don radin kansa ya ajiye mukamin.

KU KARANTA: Tsuguni bata kare ba: EFCC ta tasa keyar ‘Mamar Boko Haram’ a kan zambar N42m

Sai dai majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa Shagali ya dauki matakin yi ma takwarorinsa riga malam masallaci ne sakamakon yiwuwar su iya tsige shi a yayin zaman majalisar na ranar biyo bayan zarginsa da suke yi da nuna gazawa wajen jagoranci.

Dan majalisa mai wakiltar birnin Zazzau, Sulaiman Dabo ne ya fara bayyana Zailani a matsayin wanda ya kamata ya dare kujerar Kaakakin majalisa, yayin da Bako Kantiok na mazabar Zonkwa ya mara masa baya.

Da yake zantawa da manema labaru a fadar gwamnatin jahar Kaduna bayan wata ziyara da yan majalisar suka kai ma Gwamna El-Rufai jim kadan bayan sauyin shugabancin majalisar, Zailani yace yan majalisar ne suka amince masa.

“Ba kokawa muka yi da wani ba balleka tambayeni ya na ji bayan samun nasara, yan majalisa ne kawai suka ga dacewar yin canji, kuma suka nemi na cigaba da shugabanci, har yanzu munan nan tsintsiya madaurinki daya, kuma babu wata rikici a majalisar, kuma zamu yi ma jama’an Kaduna adalci.” Inji shi.

Sai dai da aka tambayesa ko menene dalilin da yasa tsohon kaakakin majalisar ya yi murabus, sai Zailani yace babu komai.

A wani labarin kuma, wata babbar kotun majistri dake zamanta a jahar Kano a karkashin jagorancin Alkali Aminu Gabari ta bayar da beli ga mutumin da ake tuhuma da kitsawa tare da watsa labarin auren shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministocinsa Sadiya Umar Farouk da Zainab Shamsuna.

Ana thumar mutumin mai suna Kabiru Muhammad dan shekara 32 ne laifin kirkirar labarin karya game da auren shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministar kudi Zainab Ahmad da kuma ministar kula da yan gudun hijira, Sadiya Umar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel