Majalisar dokokin jahar Kaduna ta yi dokar rage talauci a tsakanin talakawan Kaduna

Majalisar dokokin jahar Kaduna ta yi dokar rage talauci a tsakanin talakawan Kaduna

Majalisar dokokin jahar Kaduna ta kammala aiki a wata kudurin doka wanda ta kirkireshi domin kawar da talauci a tsakanin al’ummar jahar Kaduna, kamar yadda majalisar ta bayyana da kan ta a ranar juma’a.

Mataimakin kaakakin majalisar dokokin jahar, Mukhtar Isa Hazo ne ya bayyana haka yayin zaman majalisar wanda ya jagoranta a ranar Juma’a, 6 ga watan Maris, inda yace sun sauy dokar cigaban al’umma ta jahar Kaduna.

KU KARANTA: Badakalar naira biliyan 2.2: Kotu ha haramtawa hukumar yaki da rashawa bibiyan Sarki Sunusi

Majalisar dokokin jahar Kaduna ta yi dokar rage talauci a tsakanin talakawan Kaduna
Majalisar dokokin jahar Kaduna ta yi dokar rage talauci a tsakanin talakawan Kaduna
Asali: Facebook

Makasudin sauya dokar a cewar Hazo shi ne domin inganta zamantakewa tare da tattalin arzikin al’ummar jahar Kaduna, musamman yan kasa kasa ta hanyar bullo da tsare tsaren da zasu rage radadin talauci a tsakaninsu.

Hazo ya ce idan har aka fara zartar da dokar, za ta taimaka wajen karfafa ma jama’a kwarin gwiwar shiga a dama dasu a ayyukan da suka shafi al’umma, tare da tabbatar da jama’a sun bayar da kariya ga duk ayyukan da gwamnati ta musu.

Haka zalika yace dokar za ta tabbatar da an rabar da kudaden da kungiyoyi masu zaman kansu, gidauniyoyi da kuma gwamnatocin kasashen waje suka baiwa jahar, ga talakawa don rage musu talauci.

Bugu da kari majalisar ta kammala aiki a kan kudurin dokar kafa Cibiyar kula da kananan asibitoci, wanda za ta maye gurbin hukumar kula da cigaban kananan asibitoci, domin tafiyar da dukkanin al’amuran da suka shafi kananan asibitoci a duk fadin jahar.

Hazo ya ce idan aka kafa Cibiyar, za ta kafa ofisoshin a dukkanin shiyyoyin jahar Kaduna uku, wanda zasu kasance a karkashin shugabannin shiyya shiyya da za su tsara al’amuran kananan asibitoci don tabbatar sun gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

A wani labarin kuma, jam’iyyar PDP ta ga baiken sanatocin Najeriya da suka amince da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na ciyo ma Najeriya bashin dala biliyan 22.7, kimanin naira tiriliyan 8.2 kenan, inda suka ce Sanatocin sun kara ma yan Najeriya wahala.

PDP ta bayyana haka ne ta bakin sakataren watsa labarunta, Kola Ologbandiyan, wanda ya daura laifin kacokan ga Sanatocin jam’iyyar APC, ya kara da cewa abin haushin shi ne yadda Sanatocin suka amince da bashin ba tare da gwamatin ta bayar da gamsashshen bayanin yadda za ta kashe su ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel