Tofa: 'Dan Takarar Gwamnan ADC Ya Ce Zai Bar Najeriya idan APC Ta Ci Zabe a 2027
- 'Dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar ADC a Jigawa ya bayyana cewa zai bar Najeriya idan APC ta ci zaben shekarar 2027 a jihar
- Sabo Muhammad Nakudu ya ce matsalolin rashin aiki, tsaro da kuma talauci sun sa mutane ke neman sauyin gwamnati a Najeriya
- 'Dan siyasar ya bukaci matasa su shiga harkokin siyasa domin zaben shugabannin da za su kawo ci gaba da inganta rayuwar jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jigawa - 'Dan takarar gwamnan Jigawa na jam’iyyar ADC, Sabo Muhammad Nakudu, ya bayyana cewa zai bar Najeriya idan APC ta sake lashe zaben gwamna a jihar a shekarar 2027.
Sabo Muhammad Nakudu ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar shugabannin matasan jam'iyyar ADC a jihar Jigawa.

Source: Facebook
Nakudu ya hango faduwar APC a Jigawa

Kara karanta wannan
Ekiti 2026: Rigima mai zafi ta kaure tsakanin magoya bayan APC da ADC bayan an jibge kudi
Ya nuna kwarin gwiwar cewa jam’iyyarsa za ta samu nasara a zaben da ke tafe, yana mai cewa mutane da dama sun fara nuna sha’awar goyon bayan wasu jam’iyyun adawa, in ji rahoton Leadership.
A cewar Sabo Nakudu, jam'iyyar APC ba za ta ci gaba da rike mulki a jihar ba saboda yadda jama’a ke nuna rashin gamsuwa da halin rayuwa.
'Dan takarar ya ce kalaman nasa sun samo asali ne daga yadda jama’a musamman matasa ke kokawa kan matsin rayuwa da rashin ayyukan yi.
Ya bayyana cewa lokaci ya yi da ake bukatar sauyin siyasa domin kawo ci gaba ga al’umma.
'Dan takarar ADC ya tabo halin da ake ciki
Nakudu ya ce jam’iyyar ADC na da yakinin cewa za ta samu karbuwa sosai a Jigawa kafin babban zaben shekarar 2027.
Ya kara da cewa gazawar gwamnatoci wajen samar da muhimman abubuwan more rayuwa ya jefa mutane cikin damuwa da rashin tabbas game da makomarsu.
“Makonni da shekaru sun shude amma har yanzu mutane na fama da matsalar ruwa, lantarki, ilimi da tsaro,” in ji Nakudu.
Ya ce kamata ya yi a rika auna gwamnatoci ta yadda manufofinsu ke tasiri a rayuwar talakawa idan aka zo lokacin gudanar da zabe.
Dan siyasar ya bukaci matasa kada su nesanta kansu daga harkokin siyasa, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya nuna.

Source: Facebook
'Zan bar Najeriya idan....' - 'Dan takarar ADC
Ya ce dole ne matasa su shiga siyasa domin zabar shugabannin da za su kawo ci gaba da gaskiya wajen tafiyar da mulki.
“Zan bar Najeriya idan APC ta sake lashe zaben 2027. Matasa ne za su fi shan wahala idan rashin aikin yi, matsalar tsaro da rashin ingantattun ababen more rayuwa suka ci gaba,” in ji Nakudu.
Ya jaddada cewa shugabanni masu kishin ci gaban jama’a da rikon amana ne kawai ya kamata a dora wa nauyin jagoranci.
Kalaman Sabo Nakudu na zuwa ne yayin da harkokin siyasa ke kara daukar zafi gabanin babban zaben shekarar 2027.
'Yan Najeriya sun yi martani
A zantawarsu da Legit Hausa, wasu 'yan Najeriya sun yi martani ga Sabo Muhammad Nakudu kan wannan kuduri na sa.
Nura Haruna ya ce:
"Wanne ke cewa zai bar kasa idan wata jam'iyya ta ci zabe, to lallai yana da kudin da zai kula da kansa. Amma shi talaka da na abinci ke gagararsa, ai ko kauyensu ba zai iya bari ba, haka nan zai zauna ya ci gaba da fama da rayuwa.

Kara karanta wannan
Jerin jihohin da APC, APGA da sauran jam'iyyu ke mulki gabanin zaben gwamnan Ekiti
"Ya kamata 'yan siyasa su gane cewa, ba lallai sai suna kan mulki ne za su iya taimaka wa al'umma ba. Ko a anguwannin da suke, akwai mabukata, su rika taimaka wa da kudin da suke ware wa don yakin neman zabe."
Abdullahi Rabiu ya ce:
"Shi wannan na shi wasa ne. Ya na da kudin ne. Mu za mu zauna, duk yadda za ta kaya ta kaya."
Jigawa: APC ta dakatar da dan majalisa
A wani labari, mun ruwaito cewa, APC ta dakatar da 'dan Majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Auyo/Hadejia/Kafin Hausa, Hon. Usman Ibrahim tare da shugabanni.
Hakan ya biyo bayan korafe-korafen da aka shigar kansu cewa suna gudanar da wasu ayyuka da suka saba wa kundin tsarin jam'iyya.
APC ta umarci wadanda aka dakatar da su daina ayyana kansu a matsayin jami’ai ko wakilan jam’iyyar har sai an kammala bincike.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
