Karamin yaro ya mutu, wasu sun jikkata yayin da gini ya rushe dasu a kasuwar Barci

Karamin yaro ya mutu, wasu sun jikkata yayin da gini ya rushe dasu a kasuwar Barci

An shiga rudani a kasuwar barci a ranar Alhamis, 11 ga watan Maris bayan wani ginin shago ya rushe a kan wasu kananan yara dake diban karafa a baraguzan shagunan da aka rushe a kasuwar.

Daily Trust a sanadiyyar wannan tsautsayi yaro daya ya mutu nan take, yayin da wasu kuma suka samu munana rauni. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:40 na rana yayin da suke kwashe karafa da wayoyin wuta.

KU KARANTA: Mutuwa ta yi awon gaba da hadiman gwamna guda 3 cikin kwanaki 5

Karamin yaro ya mutu, wasu sun jikkata yayin da gini ya rushe dasu a kasuwar Barci

Karamin yaro ya mutu, wasu sun jikkata yayin da gini ya rushe dasu a kasuwar Barci
Source: Facebook

“Baraguzan ginin sun danne yara guda biyu, kafar daya daga cikinsu ta lalace gaba daya, daya kuma ya mutu, yayin da sauran suka jikkata.” Kamar yadda wani dan kasuwar mai suna Shehu ya bayyana.

Shehu ya bayyana cewa babu kayan aikin ceto mutanen bayan ginin ya rushe a kansu, don haka sai dai kawia jama’an dake wurin suka dinga amfani da hannu wajen kwashe baraguzan ginin da suka fadi a kan su.

Shi ma wani dan kasuwar mai suna Malam Idris ya bayyana cewa karamin yaron da hatsarin ya rutsa da shi har ya lalata masa kafa makwabcinsa ne a unguwar kwanar mai shayi dake yankin unguwar Sunusi, sunansa Daddy.

Da aka tuntubi sakataren hukumar bada agajin gaggawa na jahar Kaduna, Hajiya Maimuna Abubakar game lamarin, sai ta ce tuni ta sanar da jami’an hukumar kwana kwana domin su isa kasuwar don ganin halin da ake ciki.

Idan za’a tuna gwamnatin jahar Kaduna ta baiwa yan kasuwar kwanaki 3 su tattara inasu inasu su tashi saboda tana bukatar filin don sabunta kasuwar tare da zamanan da ita.

Wannan ne yasa yan kasuwar da kansu suka shiga rushe shagunansu domin su cire kofofinsu, karafan rodi, kwanukan sama, wayoyin wuta da sauran abubuwa masu amfani kafin gwamnati ta fara aikin rusau da kanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel