Ana Wata ga Wata: Jam'iyyar PDP Ta Takawa APC Birki kan Sauya Shekar Sheikh Pantami
- Rikicin da ya barke kan ficewar tsohon ministn sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami daga APC ya kara daukar sabon salo
- Jam'iyyar PDP reshen jihar Gombe ta yi watsi da ikirarin APC cewa har yanzu Sheikh Isa Pantami bai fita daga cikinta ba
- Jam’iyyar adawa ta ce Pantami ya yi murabus daga APC tun ranar 19 ga Mayu, 2026, kuma tana da takardun da ke tabbatar da hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe ta tsoma baki kan ce-ce-ku-cen da ake ta yi kan batun ficewar tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami daga APC.
PDP ta yi fatali da ikirarin da jam'iyya mai mulki ke yi cewa ɗan takararta na gwamna, Isa Ali Ibrahim Pantami, har yanzu mamba ne na APC.

Source: Facebook
Leadership ta ce a wata sanarwa da kakakin PDP na jihar, Abdulkadir Ahmad Dukku, ya fitar, jam’iyyar ta ce tsohon ministan ya yi murabus daga APC bisa ka’ida a ranar 19 ga Mayun 2026.
Pantami: Jam'iyyar PDP ta mallaki hujjoji
PDP ta bayyana cewa Pantami ya cika dukkan sharuddan doka da kundin tsarin mulki da ake bukata kafin shiga jam’iyyar adawa.
Jam’iyyar ta ce tana da dukkan takardun da ke tabbatar da murabus dinsa daga APC, wanda shugaban mazabarsa na lokacin ya amince da su.
“PDP tana da dukkan takardun da ke tabbatar da murabus dinsa daga tsohuwar jam’iyyarsa, wadanda shugaban mazabarsa ya karba tare da tabbatar da hakan,” in ji sanarwar.
Har ila yau, jam’iyyar PDP ta ce shugaban APC na mazabar Pantami ya amince da karbar takardar ficewar Pantami a ranar 19 ga Mayu, kuma an yada shaidar hakan a kafafen sada zumunta.
Jam'iyyar PDP ta soki APC

Kara karanta wannan
Kungiyar musulmi ta goyi bayan mafitar da Matawalle ya kawo kan matsalar tsaron Najeriya
Ahmad Dukku ya bayyana matsayar APC a matsayin abin dariya, yana mai zargin jam’iyyar mai mulki da rashin fahimtar dokokin zabe da kuma ka’idojin jam’iyya.
Ya bukaci jama’a da su yi watsi da kalaman APC, yana mai cewa jam’iyyar ta gudanar da tarukan manema labarai da dama kan batun duk da kasancewar hujjoji a fili.
Tun da farko, Kakakin APC na jihar Gombe, Moses Kyari, ya shaida wa manema labarai cewa mambobi 25 daga cikin 27 na kwamitin gudanarwar jam’iyyar a mazabar Pantami sun nesanta kansu daga takardar murabus din da ake magana a kai.
Ya kuma yi zargin cewa wani mai suna Abba Pantami ne ya kai takardar a ranar 23 ga Mayu 2026 duk da cewa an rubuta ta ne da ranar 19 ga Mayu.

Source: Twitter
PDP ta bai wa jam'iyyar APC shawara
PDP ta jaddada cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da Dokar Zabe sun ba kowa damar zabar jam’iyyar siyasa da yake so, kamar yadda Punch ta kawo.
Jam’iyyar ta bukaci APC da ta mayar da hankali kan shirye-shiryenta na zabuka masu zuwa maimakon abin da ta kira rikita-rikita marasa amfani kan batun sauya shekar Pantami.
Yadda aka fara takaddama kan Pantami
Kun ji cewa an fara takaddama kan ficewar tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami daga APC kafin komawa jam'iyyar PDP.
Yayin da bangaren Pantami ke cewa ya mika takardar fita zaga APC kafin ya shiga PDP, wasu shugabannin APC daga mazabarsa a karamar hukumar Gombe sun ce bai bi ka'ida ba.
Shugaban APC na mazabar Pantami ya ce ya karbi takardar ficewar Pantami daga jam'iyya mai mulki tun ranar 19 ga Mayu, 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

