Bayan Sulhu da Iran, Trump Ya Soki Netanyahu, Ya Zarge Shi da Babban Laifi
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya bukaci Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi sannu game da hare-hare da ya ke kai wa Lebanon
- Trump ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan amincewa da yarjejeniya da Iran domin kawo karshen takaddamar da suka yi a Gabas ta Tsakiya
- Shugaban mai shekara 80 ya nuna cewa Netanyahu na kashe fararen hula a Lebanon maimakon kai hari kai tsaye a kan 'yan kungiyar Hezbollah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kamata Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi taka tsan-tsan game da Lebanon.
Ya fadi haka ne yayin da ake fargabar cewa sabon rikicin da ya sake ɓarke wa da Hezbollah zai iya kawo cikas ga yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran.

Source: Getty Images
Donald Trump ya soki Isra'ila
Rahoton Time Magazine ya nuna cewa Donald Trump ya ce bai ji dadin yadda Isra'ila ta ke kokarin kawo karshen kungiyar Hezbollah ba.
“Ban ji daɗin yadda Isra’ila ta tafiyar da al’amuranta da Lebanon da Hezbollah ba. Ya kamata a ce sun kammala aikin cikin sauri,”
Trump ya shaida wa manema labarai a ranar Talata, yayin taron ƙasashen G7 a Faransa.
“Lamarin yana ci gaba ne ba tare da ƙarewa ba,”
In ji shi, yana nufin musayar hare-haren da ke gudana tsakanin sojojin Isra’ila da mayaƙan Hezbollah inda ya kara da cewa:
“Hakan na iya zama kalubale ga babbar yarjejeniyar, wato yarjejeniya da Iran.”
Zargin Isra'ila da kashe fararen hula
Trump ya ce yana da kyakkyawar alaƙa da Netanyahu, amma ya yi ikirarin cewa da tuni an tarwatsa Isra’ila tun da dadewa da bai sa baki ba.
Tun bayan da yaƙin Isra’ila da Hezbollah ya sake ɓarke a watan Maris, 2026, aƙalla mutum 3,783 ne suka mutu a Lebanon, yayin da 11,699 suka jikkata, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta bayyana.

Kara karanta wannan
Trump ya ballo ruwa, 'yan majalisa sun bude masa wuta kan shirin yarjejeniya da Iran
Fox News ta wallafa a X cewa Trump ya ce:
“Isra’ila ta daɗe tana yaƙi da Hezbollah kuma mutane da yawa suna mutuwa.”
Trump ya ce yana adawa da hare-haren da ke rusa gine-ginen gidajen fararen hula ke ciki, sannan ya bayyana cewa ya shawarci Isra’ila ta bar Syria ta jagoranci yaƙi da Hezbollah maimakon ta ci gaba da kai hare-hare.
Trump ya ce:
“Idan Isra’ila ba za ta iya yin aikin ba tare da kashe farar hula be, shi (Ahmed al-Sharaa) zai yi aikin. Syria za ta yi aikin.”

Source: Getty Images
Trump zai ba kasar Iran kudi
A wani labarin, kun ji cewa daga cikin yarjejeniyar da Amurka ta kulla da Iran kan tsayar da yaki akwai batun ba Tehran dala bliyan 24.
Rahotanni sun nuna cewa daftarin sulhun ya kunshi cewa Iran za ta samu akalla rabin kudin kafin kammala tattaunawar da za su fara.
Kasashen biyu sun cimma matsaya ne bayan shafe watanni suka kai wa juna hari a yakin da Amurka ta kaddamar a Iran a Fabrairun 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
