Komai Ya Fito: An Jero Abubuwa 18 da Iran da Amurka Suka Yarda da Su

Komai Ya Fito: An Jero Abubuwa 18 da Iran da Amurka Suka Yarda da Su

An samu takardar da ta ƙunshi manyan yarjeniyoyin da kasashen Iran da Amurka suka kulla domin kawo karshen yakin da suka yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Takardar da ta tanadi yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Amurka da Iran ta shiga hannun manema labarai.

Rahotanni sun nuna cewa za a yi ƙoƙarin cimma cikakkiyar yarjejeniya cikin kwanaki 60 masu zuwa domin daidaita lamura a Gabas ta Tsakiya.

Mojtaba Khamenei da Donald Trump
Shugaba Donald Trump a hagu, Mojtaba Khamenei a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yarjejeniyar sulhun Amurka da Iran

Tashar Al Arabiya ta samu kwafin takardar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran. Takardar ta ƙunshi muhimman batutuwa kamar haka:

1. Iran da Amurka da ƙawayensu sun bayyana cewa da zarar an sanya hannu kan takardar fahimtar juna, za a kawo ƙarshen yaƙi nan take kuma na har abada a dukkan fannoni, ciki har da Lebanon.

Kara karanta wannan

Yadda cimma yarjejeniya da Iran a yaƙi ya kara fito da raunin Amurka a fili

2. Iran da Amurka sun yi alƙawarin girmama ikon mallakar 'yancin yankunan juna, tare da gujewa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan juna.

3. Rahoton Bloomberg ya nuna cewa Iran da Amurka sun yi alƙawarin tattaunawa tare da cimma yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60.

4. Nan take bayan sanya hannu kan takardar fahimtar junan, Amurka za ta ɗage katangar ruwan teku da ta kakaba wa Iran.

Benjamin Netanyahu da Donald Trump
Donald Trump na tattaunawa da Benjamin Netanyahu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

5. Amurka ta kuma yi alƙawarin janye dakarunta daga yankunan da ke kewaye da Iran cikin kwanaki 30 bayan cimma yarjejeniya ta ƙarshe.

6. Bayan sanya hannu kan takardar fahimtar junan, Iran za ta ɗauki matakan gaggawa domin tabbatar da cewa zirga-zirgar jiragen kasuwanci daga Tekun Fasha zuwa Tekun Oman da akasin haka ta dawo yadda take kafin yaƙi cikin kwanaki 30.

7. Amurka ta yi alƙawari, tare da haɗin gwiwar ƙawayenta na yankin, samar da cikakken shirin farfaɗo da tattalin arziki da bunƙasa Iran.

8. Za a tsara tsarin aiwatar da wannan shiri a matsayin wani ɓangare na yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60.

Kara karanta wannan

Isra'ila za ta shiga uku, Iran ya yi mata gagarumar barazana game da Lebanon

9. Amurka ta yi alƙawarin kawo ƙarshen dukkan nau'ukan takunkuman da aka kakaba wa Iran bisa jadawalin da za a amince da shi a yarjejeniya ta ƙarshe.

Ministan harkokin wajen kasar Iran
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi a wajen wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

10. Rahoton Yahoo Finance ya nuna cewa Iran ta sake jaddada cewa ba za ta taɓa ƙera makamin nukiliya ba.

11. Iran da Amurka sun amince cewa makomar sinadaran uranium da aka tace da sauran batutuwan da suka shafi nukiliya da aka amince a kansu, za a warware su a yarjejeniya ta ƙarshe.

12. Iran da Amurka sun amince cewa kafin a kai ga yarjejeniya ta ƙarshe, za su ci gaba da riƙe halin da ake ciki yanzu: Iran za ta ci gaba da yadda shirinta na nukiliya yake, yayin da Amurka ba za ta ƙara sababbin takunkumi ga Iran ba ko kuma ta ƙarfafa dakarunta a yankin.

13. Amurka ta yi alƙawarin cewa nan take bayan sanya hannu kan takardar fahimtar juna, za ta ba da izinin fitar da ɗanyen man Iran, kayayyakin man fetur da dangoginsu, da dukkan ayyukan da suka shafe su ciki har da harkokin banki, inshora, sufuri da makamantansu.

Kara karanta wannan

Sulhu tsakanin Iran da Amurka ya fusata Isra'ilawa, sun dura kan Netanyahu

Shugaba Donald Trump dauke da bindiga
Donald Trump a wani hoto da ya yi wa Iran barazana a lokacin da suke yaki. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

14. Amurka ta yi alƙawarin cewa bisa la’akari da ci gaban tattaunawar zuwa yarjejeniya ta ƙarshe, za a saki kuɗi da dukiyar Iran da aka rike ko aka taƙaita amfani da su, kuma a ba Iran cikakken damar amfani da su.

15. Waɗannan kuɗi, ko suna cikin babban asusu ko an canja su zuwa wani wuri, za a yi amfani da su kuma za su kasance a shirye domin cikakken amfani. Amurka ta yi alƙawarin bayar da dukkan izini da lasisin da ake buƙata domin hakan.

16. Iran da Amurka sun amince cewa za a kafa wata hanyar sa ido domin tabbatar da nasarar aiwatar da yarjejeniya ta ƙarshe da kuma tabbatar da ci gaba da bin ta a nan gaba.

Shugaban kasar Iran na magana a taro
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

17. Bayan sanya hannu kan takardar fahimtar juna, kuma bayan samun tabbacin fara aiwatar da sassa na 4, 5, 10 da 11 na takardar da kuma ci gaba da aiwatar da su, Iran da Amurka za su shiga tattaunawar yarjejeniya ta ƙarshe kan sauran sassan da suka rage.

Kara karanta wannan

Trump zai ajiye gadara ya ba Iran dala biliyan 24 saboda yarjejeniya

18. Za a amince da yarjejeniya ta ƙarshe ta hanyar wani ƙuduri na musamman na kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya.

Jirgin Amurka ya yi hadari

A wani labarin, kun ji cewa Amurka ta sanar da cewa wani jirgin ta da ke kai hari da bama-bamai ya yi hadari bayan ya tashi sama daga sansanin sojoji.

Wani jami'in sojan Amurka ya bayyana cewa tun farkon hadarin da jirgin ya yi aka hararo cewa ba lallai mutanen da ke cikinsa su fito da rai ba.

Rahotanni sun nuna cewa mutane takwas ne suka mutu cikin har da sojoji, ma'aikatan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng