Jihar Imo
Sanata Uzodinma, dan takarar jam'iyyar APC, shine ya zo na hudu a zaben kujerar gwamnan jihar Imo da aka yi a shekarar 2019, kamar yadda INEC ta sanar. Masu zanga -zangar na dauke da manyan takardu da rubutattun sakonni daban - da
Har yanzu dai jam’iyyar PDP bata farfado daga hukuncin koli ta yadda ta kwace kujerar Emeka Ihedioha a matsayin gwamnan jihar Imo. Jam’iyyar PDP ta cigaba bayyana mamakinta inda ta mika wasu tarin tambayoyi a kan hukuncin da ya t
Rahotanni sun kawo cewa akwai yiwuwar hana Rev Father Ejike Mbaka na cocin Adoration Ministry yin wa'azi, idan har ya ci gaba da irin salon yadda yake gudanar da wa'azinsa da ya kauce wa tanade-tanaden akidar katolika.
Gwamnan jahar Imo, Sanata Hope Uzodinma a ranar juma’a, 17 ga watan Janairu ya zabo wasu mutanensa na hannun dama inda ya nada muhimman mukamai a jaririyar gwamnatinsa.
Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu ta sake haduwa da wani katon cikas kasa da sa’o’i 48 bayan ta rasa kujerarta na gwamna a jihar Imo.
Bayan rashin gamsuwa da yadda kotun koli ta tsige Emeka Ihedioha daga matsayin gwamnan jihar Imo, jam’iyyar People Democratic Party (PDP), ta yi kira ga sake duba lamarin cikin gaggawa da kuma janye hukuncin kotun kolin.
Wani bidiyo da ba a tabbatar ba ya billo a shafukan sadarwa inda aka nuno Sanata Rochas Okorocha na murna da waka tare da iyalansa kan zargin tsige Emeka Ihedioha daga matsayin gwamnan jihar Imo da kotun koli tayi.
Hope Uzodinma ya ce zai binciki abin da ya gudana a jihar daga 2010 zuwa yanzu. Hakan na nufin sabon Gwamna zai binciki tsofaffin Gwamnoni 3 da aka yi a Imo.
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an rantsar da Sanata Hope Uzodinma a matsayin gwamnan jihar Imo. Shugaban alkalan jihar, Justis Pascal Nnadi ne ya rantsar da zababben gwamnan da mataimakinsa, Farfesa Placid Njoku.
Jihar Imo
Samu kari