Taron Kaduna Ya Yi Albarka, Uba Sani Ya Fadi Hanyar da Za Su Saka wa Tinubu
- Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce al’ummar Arewa za su saka wa Shugaba Bola Tinubu da ƙuri’unsu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Uba Sani ya ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarori wajen gine-gine, tsaro, ilimi da noma, ciki har da ayyukan hanyoyi da sake buɗe makarantu
- Gwamnan ya buƙaci ’yan Arewa su auna Tinubu bisa ayyukansa, ba ƙabilanci ko yankin da ya fito ba, tare da gargaɗin APC kan amfani da AI
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana yadda al’ummar Arewa za su saka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Uba Sani ya ce za su saka masa da kuri'u a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Ya danganta hakan da ayyukan gwamnatin wajen inganta ababen more rayuwa, tsaro, ilimi da noma.

Source: Facebook
Uba Sani ya bayyana hakan ne ranar Asabar, yayin da yake jawabi ga magoya baya a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Kaduna, cewar Leadership.
Uba Sani ya soki masu adawa da Tinubu
Gwamnan ya kuma ƙalubalanci wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa, wanda bai ambaci sunansa ba, da ke son kayar da Tinubu, da ya gabatar da tarihin ayyukansa.
Ya jaddada cewa kasancewa ɗan Arewa kaɗai bai isa mutum ya cancanci shugabancin ƙasa ba.
Ya ce:
“Lokacin da wani ya zo gare mu yana cewa mu zaɓe shi kawai saboda shi ɗan Arewa ne, sai muka tambaye shi, ‘Za ka iya nuna mana tarihin ayyukan da ka yi?.’”

Source: Original
Uba Sani ya kare gwamnatin Tinubu
Yayin da yake kare ayyukan Tinubu, gwamnan ya tuna da ziyarar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar zuwa Birnin Gwari da ke Kaduna, ranar 27 ga Disamba, 2022. Ya bayyana yankin a matsayin wurin da matsalar rashin tsaro ta yi kamari a lokacin.
A cewar Uba Sani, Tinubu ya yi alƙawarin sake gina hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari mai tsawon kilomita 123, tare da magance matsalar tsaro a kan hanyar.
Ya ce gwamnatin tarayya ta samu gagarumin ci gaba wajen cika waɗannan alƙawura biyu.
“Yau zan iya tabbatar muku cewa alƙawura biyun da kuka ɗauka, ina farin cikin cewa kun cika su."
Sani ya kuma bayyana cewa an saki naira biliyan 100 ga kamfanin da ke aikin gina hanyar.
Gwamnan ya ƙara da cewa an sake buɗe makarantu sama da 300 da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko fiye da 150, waɗanda aka rufe a shekarar 2023 saboda matsalar tsaro.
Ya yaba da aikin sake gina babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, yana mai cewa kusan kashi 95 cikin 100 na aikin ya kammala.
Uba Sani ya karyata kashe tiriliyoyi a kamfen
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana zargin cewa Gwamna Uba Sani ya fitar da Naira tiriliyan 2.3 don ƙaddamar da kamfen APC a matsayin ƙarya.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya ce babu wani kuɗi da suka kai wannan adadi da aka ware.
Gwamnatin ta yi kira ga hukumomin tsaro da na bincike su gano waɗanda suka ƙirƙiri wasiƙar, tare da ɗaukar matakin shari’a.
Asali: Legit.ng

