Oluremi Tinubu Ta Faɗi Shirin da Ta Yi wa Rayuwarta bayan Mulki a 2031
- Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta ce tana fatan barin fadar Aso Rock a shekarar 2031, ta shiga Najeriya mafi inganci
- Ta bayyana cewa gyare-gyaren da ake samu a filayen jiragen saman Najeriya na nuna ci gaba, inda ta ce tana son jin daɗin ƙasar
- Remi Tinubu ta ƙaddamar da hedikwatar ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement a Abuja, tare da bayyana goyon bayanta ga sake zaɓen mijinta a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Uwargidan shugaban ƙasar Najeriya, Oluremi Tinubu, ta yi magana kan shirin da ta yi wa rayuwarta bayan kammala mulki.
Oluremi ta bayyana cewa tana fatan barin fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock a shekarar 2031, ta shiga Najeriya da za ta more rayuwa a cikinta yayin da take shekarunta na saba’in.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Jami'an tsaro sun mamaye wuraren da aka liƙa fastoci da allunan tallata Tinubu

Source: Twitter
Ta bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da hedikwatar ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement a Abuja, wata ƙungiya da ke gudanar da gangamin neman goyon bayan jama'a domin sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027, cewar Vanguard.
Oluremi ta yabi gyare-gyaren Tinubu
Uwargidan shugaban ƙasar ta ambaci gyare-gyaren da ake samu a filayen jiragen saman Najeriya a matsayin hujjar ci gaba, inda ta bayyana burinta na samun damar yin tafiye-tafiye cikin sauri.
Ta ce:
“Ina son barin Aso Rock a shekarar 2031, da yardar Allah, in shiga Najeriya da ni, a matsayina ta mace mai shekaru sama da saba'in, zan ji daɗin rayuwa a cikinta.
“Ina son zuwa filin jirgin sama, ina son yin tafiya cikin sauri sosai, kuma kuna iya ganin cewa filayen jiragen samanmu ma suna samun sauyi.”

Source: Facebook
Oluremi ta yaba da ci gaban da ake samu
Ta bayyana cewa Najeriya na samun ci gaba, inda ta ƙara da cewa mutanen da ba sa ganin sauye-sauyen za a iya ba su abin da ta kira “tabarau na Bola Tinubu”.
Daga bisani, Remi ta ƙaddamar da hedikwatar ƙungiyar a Abuja tare da bayyana goyon bayanta ga ƙoƙarin neman sake zaɓen mijinta, cewar Punch.
Ta ce:
“Don haka, ana samun abubuwa a Najeriya, sai dai waɗanda ba sa gani. Wataƙila za mu ba su tabarau na Bola Tinubu. Muna yin hakan, JigiBola.
“Don haka, domin ɗaukaka Allah da samun nasarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, a yanzu na ƙaddamar da hedikwatar gangamin ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement a Abuja a hukumance.”
Ta kammala jawabinta da bayyana goyon bayanta ga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma wanda ya kafa ƙungiyar, Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo.
Oluremi ta tallafa wa mutane 5,000 da jari
Mun ba ku labarin cewa uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta je wata jiha a Najeriya inda za ta ƙarfafa haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jihar.
Oluremi ta ƙaddamar da shirin tallafa wa mutane 5,000, domin rage talauci da inganta rayuwar iyalai masu buƙata.
Haka kuma, za ta ƙaddamar da Bankin Abinci na Al’umma na ƙasa a Kudu maso Gabas, sannan ta ƙaddamar da wasu ayyuka.
Asali: Legit.ng
