Yadda Gwamnatin Buhari Ta Wulakanta Tinubu duk da Sadaukarwar da Ya Yi Mata

Yadda Gwamnatin Buhari Ta Wulakanta Tinubu duk da Sadaukarwar da Ya Yi Mata

  • Laolu Akande ya bayyana yadda gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ta mayar da Bola Tinubu saniyar ware
  • Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya ce Tinubu ya zaɓi zama a APC, ya yi haƙuri har ya samu damar zama shugaban ƙasa a 2023
  • Akande ya buƙaci Atiku Abubakar ya sadaukar da burinsa na siyasa domin haɗa kan ’yan adawa, su fuskanci Tinubu a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Laolu Akande, ya bayyana yadda ake zargin gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ta mayar da Shugaba Bola Tinubu saniyar ware tare da wulaƙanta shi.

Ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sadaukar da burinsa domin haɗa kan ’yan adawa gabanin babban zaɓen 2027.

Ana zargin gwamnatin Buhari da wulakanta Tinubu
Marigayi Muhammadu Buhari lokacin da ya gana da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Da yake magana a shirin Naija Unfiltered Podcast da Vanguard ta bibiya, Akande ya ce da kansa ya shaida wasu lokuta da aka mayar da Tinubu saniyar ware a lokacin mulkin Buhari.

Kara karanta wannan

Taron Kaduna ya yi albarka, Uba Sani ya fadi hanyar da za su saka wa Tinubu

Abin da Tinubu ya fuskanta a mulkin Buhari

Akande ya ce Tinubu ya fuskanci rashin kyakkyawar mu’amala a cikin jam’iyyar APC, duk da gudummawar da ya bayar wajen ganin Buhari ya zama shugaban ƙasa a 2015.

Sai dai ya zaɓi ci gaba da zama a jam’iyyar yana jiran lokacinsa, maimakon ya fice.

Ya ce:

“Me ba su yi wa Tinubu ba? Ku gaya mini, me ba su yi ba? Ko tsakanin 2015 da 2023, an mayar da mutumin saniyar ware. Na gani da idona tsab, na zauna a tarurruka inda suka sanya Bola Ahmed Tinubu a bayana.”

A cewarsa, Tinubu bai bari yadda aka mu’amalanta da shi ya sa ya fice daga APC ba. Maimakon haka, ya yi haƙuri tare da ci gaba da shirya harkokinsa na siyasa har ya samu nasarar maye gurbin Buhari a 2027.

Ya kuma yi tsokaci kan takaddamar da ta biyo bayan sauya fasalin takardun kuɗin naira gabanin zaɓen 2023, yana mai cewa Tinubu ya tunkari ƙalubalen siyasar ta hanyar tattara magoya baya, maimakon ya yi watsi da burinsa.

Kara karanta wannan

Yadda 'yunwa' za ta ruguza lissafin Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027

Wahalar da Tinubu ya sha a mulkin Buhari
Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Hoto: Garba Shehu.
Source: Twitter

Akande ya kare APC kan zarge-zarge

Akande ya yi watsi da zargin cewa APC mai mulki ce ta haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin shugabannin ’yan adawa ya ce dole ne jam’iyyun adawa su iya jure matsin lamba daga jam’iyyar da ke kan mulki.

“Ba na cewa hakan daidai ne, amma haka suka yi. Don haka, idan da gaske kuke a matsayin ’yan adawa, dole ne ku iya jurewa ku kai ga nasara ta hanyar yin abin da ya kamata."

- Akande

Tsohon hadimin shugaban ƙasar ya danganta wasu matsalolin ’yan adawa da son kai, yana mai cewa Atiku ne ya kamata ya ɗauki matakin farko wajen haɗa kan masu adawa da Tinubu.

Ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kasance a shirye ya ajiye burinsa na kansa domin cimma muradin ’yan adawa baki ɗaya.

Akande ya ƙara da cewa irin wannan mataki zai iya ƙarfafa ’yan adawa wajen tsara haɗin kai domin ƙalubalantar jam’iyyar da ke mulki.

Kara karanta wannan

Atiku ko Tinubu: An raba gardama kan dan takarar da ya fi dacewa ya zama shugaban kasa

Ya kuma tuna cewa, duk da rawar da Tinubu ya taka wajen ganin Buhari ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na APC a 2015, an ƙi amincewa da wasu mutanen da aka ce ya ba da shawarar naɗa su ministoci.

Ya kara da cewa:

“An zaɓi Alake, an zaɓi Edun. Amma suka je suka zaɓi waɗanda bai ba da shawarar naɗawa ba, domin kawai su nuna cewa ba zai iya tilasta mana abin da za mu yi ba."

APC ta caccaki Atiku kan 'yada' karya

A wani labarin, an ji cewa jam’iyyar APC ta zargi Atiku Abubakar da ADC da shirin amfani da bidiyoyin bogi da takardun ƙarya domin ɓata taron kamfen ɗinta a Kaduna.

Kakakin kwamitin kamfen APC, Dele Alake, ya ce an ƙirƙiri wasiƙar bogi da ke zargin gwamnatin Kaduna da kashe naira tiriliyan 2.3 wajen taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.