Tashin hankali: Mata ta yankewa mijinta harshe, hanci ta kuma kira mahaifiyarshi ta zo ta dauki gawarshi

Tashin hankali: Mata ta yankewa mijinta harshe, hanci ta kuma kira mahaifiyarshi ta zo ta dauki gawarshi

Rahotanni sun kawo cewa an kwantar da wani likita, Cherechi Okonko a sashin bayar da agajin gaggawa na cibiyar lafiya ta tarayya, Owerri, jahar Imo, kan raunukan da matarsa ta ji masa.

An tattaro cewa matar, wacce ta kasance ma’aikaciyar jinya ta cire wa mijin nata hakorin sama, saman harshensa da kuma wani sashi na dasashinsa na kasa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ma’auratan na zama ne a yankin World Bank da ke babbar birnin jahar.

An kwashi mijin nata wanda ya kasance likitan mata a asibitin FMC Owerri zuwa asibitin inda likitoci suka ta gwagwarmayar ganin sun ceto rayuwarsa.

An tattaro cewa ya shiga cikin mawuyacin hali inda daya baya ya dawo hankalinsa.

Tashin hankali: Mata ta yankewa mijinta harshe, hanci ta kuma kira mahaifiyarshi ta zo ta dauki gawarshi
Tashin hankali: Mata ta yankewa mijinta harshe, hanci ta kuma kira mahaifiyarshi ta zo ta dauki gawarshi
Asali: Instagram

Wani ma’aikacin FMC Owerri da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Wata mata ta ci zarrafin wani likitan FMC Owerri a daren jiya bayan sun samu wani sabani."

Ya ce, “matar ta yanke masa hancinsa, hakoran sama, saman harshensa da kuma dasashinsa na kasa. Sannan ta kira mahaifiyar yaron kan ta zo ta dauki gawar danta.

“Likitan ya yi sa’a, domin an kai shi asibiti cikin gaggawa a daren jiya sannan aka daidaita shi. Koda dai ya dawo hayyacinsa, ba zai iya magana ba domin yana sanye da abun numfashi."

KU KARANTA KUMA: Gargadi: Yawan shan Paracetamol na iya kashe mutum - Ma'aikaciyar lafiya ta gargadi 'yan Najeriya

Kakakin yan sandan jahar, Orlando Ikeokwu ya bayyana cewa an kawo way an sanda rahoton lamarin.

A wani labarin kuma mun ji cewa wata coci a Najeriya ta ki yin bikin birne wani marigayi a cocin saboda ya kai shekaru uku baya zuwa cocin kuma baya bada sadaka na tsawon lokacin da ya dauka baya zuwa bautar.

Kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito, wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta tuwita mai suna Kelvin Odanz ne ya wallafa labarin amma bai bayyana kowacce coci bace.

Labarin kuwa ya jawo cece-kuce a kafar daga mutane da dama wadanda suka ce wannan aikin cocin orthodox ne.

Kelvin ya ce mamacin ya kasance mahaifin daya daga cikin abokan aikin shi ne. Ya kara da cewa, cocin ta jaddada cewa sai iyalan mamacin sun biya kudin da bai biya ba na shekaru uku kafin su karbi gawar shi don birne shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel