Tinubu na Ta Shirin Kamfe, 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane kusan 40

Tinubu na Ta Shirin Kamfe, 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane kusan 40

  • An tabbatar da mutuwar mutane aƙalla 37 bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a jihar Taraba
  • Maharan sun buɗe wuta kan jama’a, sun kwashe kayan abinci daga shaguna tare da cinna wa gidaje da shaguna wuta
  • Rundunar ’yan sandan Taraba ta ce an tura ƙarin jami’an tsaro, ciki har da sojoji da rundunonin ’yan sanda na musamman, domin hana sake kai hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Taraba - Akalla mutane 37 sun mutu bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari kan al’ummar Binnari da ke ƙaramar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.

Maharan, waɗanda rahotanni suka ce suna da yawa, sun shiga garin ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026.

'Yan bindiga sun yi kisa a Taraba
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas Hoto: @AgbuKefas
Source: Twitter

'Yan bindiga sun kai hari a Taraba

Rahoton tashar Channels tv ya ce 'yan bindigan sun riƙa harbe-harbe ba kakkautawa, kwashe kayan abinci daga shaguna tare da ƙona gidaje da wuraren kasuwanci.

Kara karanta wannan

"Ba za mu yarda ba"; 'Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi karfinsu a Zamfara

Rahotannin farko daga garin sun bayyana cewa mutane 10 ne suka mutu. Sai dai daga baya, shugabannin al’umma da matasa sun gudanar da bincike a dazuzzuka da kogunan da ke kewaye da garin, inda suka gano ƙarin gawarwaki har adadin waɗanda suka mutu ya kai 37.

Ana zargin maharan sun shigo jihar Taraba ne daga jihar Filato da ke maƙwabtaka da ita. Ƙaramar hukumar Karim Lamido tana da iyaka da jihohin Adamawa, Bauchi, Gombe da Nasarawa.

’Yan sanda sun tabbatar da harin

Rundunar ’yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da harin a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Victor Mshelizah, ya fitar ranar Asabar, 24 ga watan Oktoban 2026.

A cewar sanarwar, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana, jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a, jaridar Premium Times ta kawo rahoton.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Rundunar ’yan sandan jihar Taraba na cikin alhinin sanar da jama’a game da harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai kauyen Binnari ranar 23 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 15:00, jim kaɗan bayan sallar Juma’a.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yan bindiga sun rutsa shugaban matasan APC da matarsa a cikin gida

Rundunar ta ƙara da cewa maharan sun shiga kauyen suna harbe-harbe, inda suka kwashe kayan abinci daga shaguna, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici.

An miƙa gawarwaki ga iyalan mamatan

’Yan sandan sun ce bayan samun rahoton harin daga jami’in da ke kula da yankin Binnari, an gaggauta tura jami’ai zuwa wurin da lamarin ya faru.

Jami’an sun gano gawarwaki 10 masu raunin harbin bindiga, waɗanda daga bisani aka miƙa wa iyalansu domin yi musu jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.

Sai dai binciken da shugabannin al’umma da matasa suka ci gaba da yi a dazuzzuka da kogunan yankin ya kai ga gano ƙarin gawarwaki, wanda ya ƙara yawan waɗanda suka mutu zuwa 37.

An kara tsaurara tsaro a yankin

Rundunar ’yan sandan ta ce ta sanya ƙarin jami’ai cikin shirin ko-ta-kwana, tare da tura tawagogin haɗin gwiwa zuwa yankin domin hana sake kai hare-hare.

Tawagogin sun haɗa da jami’an sassan musamman na ’yan sanda, rundunar ’yan sanda ta Mobile Force, sauran jami’an ’yan sanda, sojojin Najeriya da wasu hukumomin tsaro.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Taraba
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Mutanen gari sun kashe 'yan bindiga

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki ayarin motoci a Sokoto, an kashe malami da wasu mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa mazauna garin Birnin Tudu da ke Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara sun ce sun kashe ’yan bindiga sama da 30. .

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun zo da ɗaruruwan babura, suka kewaye ƙauyen sannan suka fara harbe-harbe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng