Bidiyon yadda wata mata ta antayawa mijinta soyyayen mai a baya saboda zafin kishi

Bidiyon yadda wata mata ta antayawa mijinta soyyayen mai a baya saboda zafin kishi

Kasa da sa’o’i 24 bayan da ‘yan sandan jihar Imo suka cafke wata mata da laifin yunkurin kashe mijinta ta hanyar soka masa wuka har sau biyu yayin baccinsa, sai ga wata sabuwa ta bullo.

Kamar yadda ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook mai suna Chinonso Chibuogwu yace, mahaifin yara hudun ya kira shi wajen karfe dayan dare da cewa ya gagauta zuwa gidansa, kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito.

Kamar yadda Chinonso ya bayyana, abokin nashi mai suna Michael Amajuoyi ya dawo gida ne da dare. Ya tube don zuwa yin wanka a bandaki ne inda mata tashi ta tarar dashi.

Tuni dama matar tashi tana zarginsa da cin amanarta amma sai a ranar ta tabbatar. Bayan barin wayarsa da yayi a falo, wani sakon kar-ta-kwana ya shigo wayar. Babu bata lokaci kuwa ta shiga madafi inda ta soya man girki wanda tayi amfani da shi wajen watsawa mijin a baya.

DUBA WANNAN: PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari

Kamar yadda Chinonso Chibuogwu ya wallafa, “A tunanina wasa ne dai kamar yadda muka saba. Michael Amajuoyi wanda ke zama a Nnaze da ke Owerri ne ya kira ni yana ihu tare da hargowar cewa zai mutu. Abinda yake cewa kawai shine ‘kazo kawai, zan mutu’."

“Dole ce ta sani na dau mota na fita da karfe daya da rabi na dare zuwa gidansa. Ina isa kuwa na saka shi a mota inda muka garzaya asibiti saboda dai a kone na ganshi." ya kara da cewa.

“Daga baya ne yake sanar dani cewa dama tun farko matarsa na zarginsa amma bata tabbatar ba. A yau kuwa ya dawo can dare ne sai ya bar wayarsa a falo inda ta samu damar dauka ta ga sakon wata. ‘Ina godiya masoyina a kan sabuwar wayar da ka siyo min. Na dade ina mafarkin mallakar irinta. Mu kwana lafiya kuma ka kula da kanka.’ Wannan ne ya harzuka matar har ta kwara masa tafasasshen mai a baya.” cewar abokin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel