Innalillahi wa inna ilaihirraji'un: An halaka wani jigon APC

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un: An halaka wani jigon APC

- Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta cafke wani mai magani da ma'aikatansa a kan zargin kisan kai

- Kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya sanar, lamarin ya auku ne a yankin Umuguma na birnin Owerri

- Mai siyar da maganin da ma'aikatansa sun yi wa jigon APC din mugun duka ne saboda ya je tsayar da motarsa a gaban shagonsu

Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta tabbatar da kama wani mai hada magani da ma'aikatansa a kan zargin yi wa wani mutum dukan mutuwa a Owerri.

Mai magana da yawun rundunar, SP Orlando Ikeokwu, ya ce lamarin ya faru ne a yankin Umuguma da ke birnin Owerri din.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa, mutumin da aka kashe mai suna Damian Ali, jigo ne a jam'iyyar APC. Mai shagon siyar da maganin ne tare da ma'aikatansa suka halaka shi.

DUBA WANNAN: Daga karshe: Jonathan ya bayyana dalilin sauke Farida Waziri

An gano cewa, Ali dan asalin Nkarahu ne da ke karamar hukumar Ohaji/Egbema da ke jihar Imo. Yayi yunkurin tsayar da motar shi ne a gaban shagon siyar da magungunan ne wanda hakan ya jawo hayaniya tsakanin shi da mamallakin shagon.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce an kama mai siyar da maganin tare da ma'aikatansa don amsa tambayoyi. An kuma tura 'yan sanda daga cikin rundunar don kwantar da tarzoma a yankin. Ya ce da kanshi mai maganin ya kai kanshi gaban 'yan sanda.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Olaniyi Fafowora ya bada umarnin aiwatar da gamsasshen bincike a kan lamarin.

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un: An halaka wani jigon APC
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un: An halaka wani jigon APC
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel