Kungiyar Biyafara ta ce dole Uzodinma ya sauka daga Gwamnan Imo

Kungiyar Biyafara ta ce dole Uzodinma ya sauka daga Gwamnan Imo

A Ranar Talata, 4 ga Watan Fubrairun 2020, Kungiyar Biafra Zionists Federation, ta fito ta na cewa ya zama dole gwamna Hope Uzodinma ya sauka daga mulki.

Bayan kwana 20 da zamansa gwamna, wannan kungiya ta ba Hope Uzodinma makonni biyu, ya bar kan karagar mulki kamar yadda Jaridar The Nation ta rahoto.

Kungiyar Tawayen ta yi wannan kira ne ta bakin shugabanta, Benjamin Onwuka, wanda ya fito ya na cewa ba za su marawa gwamnatin Uzodinma baya a Imo ba.

A cewar Mista Benjamin Onwuka, ba halatacciyar gwamnati ke mulki a jihar Imo ba. “Wanda ya gaza lashe zaben ko da karamar hukuma guda ba zai yi mulki ba.”

“Jihar Imo ta na cikin kasar Biyafara, kuma a dalilin haka, babu wani Sojan gona da zai fado daga sama ya zo ya fara mulkar jama’a a jihar Imo.” Inji kungiyar ta BZF.

KU KARANTA: Magoya bayan Gwamnan Imo da aka tsige su na zanga-zanga

Kungiyar Biyafara ta ce dole Uzodinma ya sauka daga Gwamnan Imo
Kotun koli ta tsige Emeke Ihedioha ta ce Hope Uzodinma ne Gwamnan Imo
Asali: UGC

Onwuka ya kuma bayyana cewa abin da ke faruwa a jihar Imo a halin yanzu, ya shafi kowane mutumin Ibo. Wannan ya sa ya ke neman goyon bayan jama’a.

“Mu na da labari daga majiya mai mai karfi cewa an kawo Uzodinma ne saboda kwangilar musuluntar da Imo da kafa Ruga. Amma ba za a cin ma wannan ba.”

Jawabin na shugaban kungiyar Biyafaran ya ce: “Ya da makonni biyu, ya sauka daga mulki, ya ba ainihin Mai kujerar, Emeka Ihedioha damar karasa wa’adinsa.”

Bayan barazana ga Mai girma gwamnan, Biafra Zionists Federation, sun gargadi ‘Yan majalisar dokokin jihar Imo da ke sauya-sheka, da cewa za su yi da-na-sani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel