'Duk kun rasa kujerunku' - PDP ta yi magana a kan mambobinta da suka koma APC a Imo

'Duk kun rasa kujerunku' - PDP ta yi magana a kan mambobinta da suka koma APC a Imo

Shugabancin jam'iyyar PDP na kasa ta bayyana cewa duk mambobinta takwas da suka sauya sheka a ranar Talata a majalisar jihar Imo zuwa jam'iyyar APC sun rasa kujerunsu.

A wata takardar da mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar, ya ce masu sauya shekar ba zasu iya ci gaba da rike kujerunsu ba tunda jama'a sun yarje musu ne a karkashin jam'iayyar PDP din.

'Yan majralisar wadanda suka hada da kakakin majalisar, sun sanar da sauya jam'iyyarsu ne a zauren majalisar jihar a ranar talata, ci gaban da jam'iyyar PDP ta duba da son kansu, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Jam'iyyar ta kwatanta abinda 'yan majalisar suka yi da rashin kishi tare da cin amanar jama'ar mazabunsu wadanda suka zabesu a karkashin jam'iyyar PDP don su wakilce su.

"Masu sauya jam'iyyun sun nuna tsantsar rashin dabi'a, rashin iya mulki a lokutan kalubale da kuma rashin imanin tsayuwa tare da jama'arsu.

'Duk kun rasa kujerunku' - PDP ta yi magana a kan mambobinta da suka koma APC a Imo
'Duk kun rasa kujerunku' - PDP ta yi magana a kan mambobinta da suka koma APC a Imo
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Kano: Dan takarar PDP da ya kayar da Abdulmumi Kofa yana shirin koma wa APC

"Wadannan masu sauya jam'iyyar sun san irin abinda aikinsu zai jawo musu. Sun rasa kujerunsu da kuma zamansu 'yan majalisar jihar Imo. Saboda sai ta karkashin inuwar jam'iyyar da jama'a suka zabesu ne zasu iya cigaba da mulkinsu.

"Wannan bayyananne ne a kundin tsarin mulki na 1999 cewa, duk wani dan majalisar da ya canza jam'iyyar da aka zabe shi don wakiltar mutane, toh ya rasa wannan kujerar don kujerar mallakin jam'iyyar da aka zabesa ne ba shi ba," Ologbondiyan ya ce.

Mai magana da yawun jam'iyyar ya kara bayyana cewa, barin kujerar duk wanda ya sauya sheka zuwa wata jam'iyya na nan daram a sashi na 109 sakin layi na daya na kundin tsarin mulki na 1999.

Kakakin jam'iyyar PDP din ya ce basu da wani zabi da ya wuce su umarci hukumar zabe mai zaman kanta da ta hada wani sabon zabe don maye gurbin 'yan majalisar da suka sauya shekar zuwa jam'iyyar PDP

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel