Tirkashi: Bidiyon yadda aka sha dambe tsakanin DPO na 'yan sanda da wani a bainar jama'a

Tirkashi: Bidiyon yadda aka sha dambe tsakanin DPO na 'yan sanda da wani a bainar jama'a

- Wani bidiyon DPO na shan dambe da matukin keke napep ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani

- A cewar matar da ta nadi bidiyon, matukin napep din ne ya bata wa DPO motar shi, amma sai DPO ya bukaci N7,000 don gyara

- Mawallafin bidiyon ya ce lamarin ya faru ne a Uratta da ke karamar hukumar Owerri ta Arewa a jihar Imo

Kwanaki 15 bayan wasu fusatattun mutane sun hana dan sanda kama wani, wani bidiyon mai keke napep da DPO suna dambe ya bazu a yanar gizo.

Jaridar Within Nigeria ta gano cewa DPO din 'yan sandan ya zagi matukin keke napep saboda zargin da yayi mishi na bata motar shi.

A cikin bidiyon wanda ma'aboci amfani da Facebook mai suna Frankline Tonichukwu Ibe ya wallafa, DPO din dai na Uratta ne da ke karamar hukumar Owerri ta Arewa.

Kamar yadda mutanen yankin suka ruwaito, matukin keke napep din ya bata wa dan sandan mota ne wanda hakan ya jawo cacar bakin da ta kai su ga dambe. Dan sandan yayi yunkurin kama matukin keke napep din ne don kai shi ofishinsu.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sanya matan Hausawa ke tsufa da zarar sunyi aure

Wata mata wacce ba ta bayyana sunanta ba ta ce DPO din ya bukaci matukin napep din da ya ba shi N7,000 don ya gyara motar shi. Rashin bayar da kudin ne ya jawo wannan fadan.

A bidiyon mai mintina biyu, an ji matar na ihun cewa DPO na fada da mutumin amma jim kadan sai aka ji harbin bindiga tare da ganin mutane na yunkurin kaiwa yaron dauki. Daga nan ne 'yan sanda biyu suka bayyana tare da damke matukin keke napep din.

Kamar yadda mawallafin bidiyon ya rubuta; "Abin kunya ga 'yan sandan Najeriya. DPO din Uratta da ke karamar hukumar Owerri ta Arewa ne ke dambe da matukin keke napep a kan ya bata mishi motar shi. Wannan ne ire-iren 'yan sandan da ke kare rayukan 'yan jihar Imo. A Najeriya kadai hakan ke faruwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel