Yadda al’umma suka rushe gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane

Yadda al’umma suka rushe gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane

Al’ummar garin Uratta na karamar hukumar Owerri ta Arewa na jahar Imo sun rushe gidaje guda uku mallakin wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, Okechukwu Uche biyo bayan mutuwar matar babban basaraken garin, Uwargida Ugoeze Comfort Okoro.

Daily Trust ta ruwaito a yanzu haka Uche yana gidan yari na jahar Imo, amma jama’an garin sun tabbatar da cewa shi ne ya shirya yadda aka yi garkuwa da matar Sarkinsu, ma shekaru 76 a rayuwa, wanda daga bisani aka kasheta bayan an biya kudin fansa.

KU KARANTA: Hukuncin kisa: Maryam Sanda ta kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara

Yadda al’umma suka rushe gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane
Yadda al’umma suka rushe gidan wani kasurgumin mai garkuwa da mutane
Asali: Facebook

Wannan ne ya harzuka jama’an suka fuskanci gidajen Uche a fusace har sai da suka sauke dukkaninsu guda uku daga sama har kasa.

Ita ma rundunar Yansanda reshen jahar Imo ta bayyana Uche a matsayin wanda ya shirya kisan matar, amma sun musanta hannu cikin rusa gidajensa, kamar yadda kaakakinta, Orlando Ikeokwu ya bayyana.

Okeokwu ya bayyana cewa rundunar ta kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu cikin garkuwa da uwargida Comfort a yayin da suka tafi amsan cikon kudinsu, kuma sun tabbatar da cewa Uche ne jagoransu.

Mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Imo ya kara da cewa sun kwato bindigu guda biyu daga hannun miyagun, bindigun da yace mallakin wasu Yansanda ne da yan bindigan suka kashe a shekarar da ta gabata bayan sun kai musu harin kwantan bauna.

Sakamakon kisan uwargida Comfort, a yanzu haka al’ummar garin sun dakatar da duk wasu bukukuwan gargajiya da aka saba yi a garin domin nuna alhininsu game da mutuwarta, tare da nuna girmamawa a gare ta.

Shugaban kungiyar cigaban garin Uratta, UDA, Mista Canice Madukaji ya bayyana ma manema labaru cewa sun shiga damuwa da bakin ciki biyo bayan kisan uwargida Comfort, don haka sun dakatar da bikin gargajiya na ‘Onwa Oru’ da za’a gudanar a ranar 22 ga watan Feburairu.

Canice yace sun dauki wannan mataki ne bayan ganawa da majalisar sarakunan gargajiya na garin da sauran masu ruwa da tsaki. Daga karshe yace zasu cigaba da bayar da goyon baya ga gwamnatin jahar Imo da hukumomin tsaro don ganin an hukunta wadanda suka tafka wannan laifi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel