Ihedioha: Jami’iyyar PDP ta bada umarnin azumin mako guda a Imo

Ihedioha: Jami’iyyar PDP ta bada umarnin azumin mako guda a Imo

Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Imo, ta bayyana cewa za a fara azumin mako guda domin a dawowa mata da kujerar gwamna da aka karbe a hannun Emeka Ihedioha.

PDP ta kaddamar da wannan azumi na kwanaki bakwai ne a Ranar Asabar, 8 ga Watan Fubrairun 2020. Sakataren jam’iyya na jiha, Nze Ray Emeana, ya bayyana wannan.

Ray Emeana ya shaidawa Duniya cewa za a soma wannan azumi ne daga yau Lahadi, 9 ga Watan Fubrairu. Hakan na nufin za a kammala azumin a karshen makon gobe.

Bugu da kari, Mista Nze Ray Emeana, ya yi kira ga ‘Ya ‘yan jam’iyyar da su rika sa bakaken tufafi a lokacin da su ke wannan azumi domin nuna takaicin da su ke ciki a jihar.

Jawabin jam’iyyar ya ce: “A wannan lokaci, duka shugabannin mazabu su tara jama’a a cocin da ke kananan hukumomi, su rika addu’a kullum da rana da kuma buda-baki.”

KU KARANTA: An kama wani Mawakin Kwankwasiyya a Jihar Kano

“Abin da za a roka shi ne Ubangiji ya shiga lamarinmu, ya ba Emeka Ihedioha nasara a matsayin ainihin zababben gwamnan jihar Imo.’ Inji Sakataren jam’iyyar ta PDP.

“Mu na kira ga mutanen Imo su zauna lafiya, su dage da addu’o’i, yayin da mu ke jiran kotun koli su duba lamarin karar da Emeka Ihedioha ya shigar kan zaben gwamna.”

Ku na da labari cewa baya kotun koli ta ruguza nasara Emeka Ihedioha, inda ta ce ‘Dan takarar APC, Hope Uzodinma ya ne ya lashe zaben gwamnan jihar Imo a 2019.

Ihedioha ya sake hayar sababbin Lauyoyi 30 ya na neman kotun koli ta sake duba shari’ar da ta yi. Kanu Agabi da wasunsu su na so kotu ta dawo ta ba PDP gaskiya a shari’ar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel