'Yan Najeriya Sun Yi Magana da Murya Ɗaya kan Sake Zaben Tinubu a Babban Zaben 2027

'Yan Najeriya Sun Yi Magana da Murya Ɗaya kan Sake Zaben Tinubu a Babban Zaben 2027

  • Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce ’yan Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu
  • Yilwatda ya ce mata da matasa na farin ciki da shugabancin Tinubu, yana mai cewa jam’iyyun Accord, PDP da APGA sun haɗa kai da APC
  • Ya bayyana cewa APC za ta dogara kan ayyukan gwamnatin Tinubu, gyare-gyaren da take yi da kuma shirinta na samar da makoma mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce ’yan Najeriya sun bayyana matsayarsu a sarari kuma cikin murya ɗaya cewa za su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shekara mai zuwa.

Yilwatda ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Kaduna.

Kara karanta wannan

Yadda 'yunwa' za ta ruguza lissafin Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027

Nentawe.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @Nentawe
Source: Facebook

A rahoton Leadership, Farfesa Yilwatda ya kuma ce mata da matasa na farin ciki da shugabancin Tinubu, kuma suna samun ƙwarin gwiwa daga gare shi.

“Mai girma shugaban ƙasa, al’umma sun bayyana matsayarsu, kuma muryarsu a bayyane take. ’Yan Najeriya na farin ciki, matanmu na farin ciki, matasanmu na farin ciki, kuma al’umma na samun ƙwarin gwiwa daga shugabancinka.
“Yau muna bikin jagora mai ƙarfin hali, wanda ya nuna ƙudurin ɗaukar matakai masu wahala amma wajibi domin amfanin ƙasarmu,” in ji shi.

Yilwatda ya bayyana cewa jam’iyyun Accord, PDP da APGA sun haɗa kai da APC domin tabbatar da nasarar Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa mafi ƙwarewa kuma abin amincewa da shi.

“Muna alfahari da gabatar wa ’yan Najeriya ɗan takarar shugaban ƙasa mafi ƙwarewa kuma abin amincewa da shi. APC tana da haɗin kai, a shirye take, kuma tana da kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

APC ta gane tasirin Arewa, ta faɗi ƙarfin ikon talakawa, ƴan siyasar yankin

Yilwatda ya lura cewa yaƙin neman zaɓen APC zai dogara ne kan ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gudanar, gyare-gyaren da take ci gaba da yi da kuma kyakkyawan hangen nesanta game da makomar ƙasar.

Ya buƙaci ’yan Najeriya su tantance gwamnati ba wai ta la’akari da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta kawai ba, har ma da ƙarfin halin da ake buƙata wajen magance matsalolin tsarin ƙasa da suka daɗe suna addabar ta.

A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta nuna aniyarta wajen tunkarar mawuyacin halin tattalin arziki, ƙarfafa ababen more rayuwar ƙasa da kuma sake tsara tattalin arzikin domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa alfanun gyare-gyaren da ake yi za su ƙara fitowa fili yayin da ake ci gaba da aiwatar da su.

Shugaban APC na ƙasa ya jaddada cewa wa’adin farko na Tinubu ya kafa tubalin da gwamnatin wa’adi na biyu za ta iya ginawa domin samar da Najeriya mai wadata, tsaro da kuma haɗa kowa da kowa.

Tinubu ya zargi yan adawa

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya zargi jam’iyyun adawa da haddasa yunwa da talauci a Najeriya, yayin da ya kaddamar da yakin neman zabensa a Kaduna.

Ya kuma yi wa magoya bayansa alkawarin samun wadata idan aka sake zabensa, yana mai tabbatar musu cewa ba za su yi nadamar sake ba shi wa’adi na biyu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262