Uzodinma ya ziyarci Buhari, ya mika wata babbar bukata gabansa

Uzodinma ya ziyarci Buhari, ya mika wata babbar bukata gabansa

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma a ranar Alhamis ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya bukaci taimakonsa wajen dawo da wasu kudi har biliyan talatin da biyu ga jihar wanda gwamnan da ya shude ya kashe wajen yin titunan gwamnatin tarayya a jihar.

A yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati bayan taron da yayi da shugaban kasar, Uzodinma ya ce jihar Imo na cikin halin rashin kudi, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Ya ce idan aka saki kudaden, za a yi amfani dasu ne wajen biyan albashin ma’aikata da kuma biyan ‘yan fansho hakkokinsu.

Ya ce wadanda ya tuntuba sun gano cewa a kalla an kashe naira biliyan talatin da biyu a baya wajen yin titunan gwamnatin tarayya a jihar.

Uzodinma ya bayyana cewa, ya yi wa Buhari bayani dalla-dalla na halin da jihar ke ciki. Ya kara da cewa Shugaban kasar ya matukar saurararsa.

DUBA WANNAN: Arewa na halaka kanta da kanta - Sarki Sanusi II

Uzodinma ya ziyarci Buhari, ya mika wata babbar bukata gabansa
Uzodinma ya ziyarci Buhari, ya mika wata babbar bukata gabansa
Asali: Twitter

Karin bayani na nan tafe...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164