Zanga-zanga: Uzodinma ya ce manyan Ibo a PDP su na neman ganin bayan Gwamnati

Zanga-zanga: Uzodinma ya ce manyan Ibo a PDP su na neman ganin bayan Gwamnati

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, ya jefi manyan shugabannin Ibo da ke cikin jam’iyyar PDP da yunkurin ganin bayan gwamnatin shugaba Buhari.

Hope Uzodinma ya ke cewa wasu manyan kabilar Ibo ne kan gaba wajen ganin an kifar da gwamnati mai-ci wanda Muhammadu Buhari ya ke jagoranta.

Sanata Hope Uzodinma ya yi wannan ikirari ne a lokacin da ya ke maida martani game da zanga-zangar da jam’iyyar hamayya ta shirya bayan ya samu mulki.

Mai girma Uzodinma ya samu mulki ne bayan da kotun koli ta ruguza nasarar PDP a zaben 2019. Wannan ya sa wasu ‘Yan adawa su ka gudanar da zanga-zanga.

Gwamnan na Imo ya ke cewa ya fahimci manyan shugabannin Ibo su ne ‘yan gaba-gaba wajen gudanar da wannan zanga-zanga da jam’iyyar PDP ta shirya.

KU KARANTA: Jonathan ya yi magana game da matsalar rashin tsaro a Najeriya

Zanga-zanga: Uzodinma ya ce manyan Ibo a PDP su na neman ganin bayan Gwamnati
Sanata Hope Uzodinma ya soki 'Yan adawan da ke neman kawo matsala
Asali: UGC

Sabon gwamnan ya ce sauran shugabanni daga bangarorin Najeriya ba su cikin wannan zanga-zanga da aka yi wa kotun koli, sai dai manyan kasar Ibo kurum.

A cewar gwamnan na APC, ana neman labewa ne da wannan zanga-zanga da aka shirya domin a kifar da gwamnatin tarayya, inda ya koka da wannan lamarin.

Sanata Uzodinma ya nuna cewa Ibo su na neman jefa kansu a cikin hadari da biyewa wannan shiri da aka dauko na gogawa hukumar zabe bakin jini a boye.

‘Zanga-zangar nan shiri ne da aka kitsa mai kama da Revolution Now, domin kifar da gwamnati, abin takaici ne wasu manyan Ibo sun fadawa wannan aiki.”

“Abin kunya ne ace saboda rashin kishi, shugabannin Ibo su na gayyatar wasu su shigo Najeriya su shiga cikin harkokinmu domin jawo sabani.” Inji Gwamnan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng