Tashin Hankali: Jirgin Sama Ya Gamu da Matsalar Na'ura bayan Tashi daga Abuja

Tashin Hankali: Jirgin Sama Ya Gamu da Matsalar Na'ura bayan Tashi daga Abuja

  • Jirgin saman Air Peace da ya taso daga Abuja zuwa Asaba ya yi saukar gaggawa a Legas bayan rahotannin samun matsalar fasaha a tsakiyar tafiya
  • An karkatar da jirgin zuwa Legas ne bayan an samu matsala a ɗaya daga cikin na’urorinsa
  • Har yanzu babu cikakken bayani kan irin matsalar da ta faru, halin da fasinjoji suke ciki ko ko kamfanin ya shirya wani jirgin domin kai su Asaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - An kauce wa wani abin da ka iya zama babban haɗarin jirgin sama bayan wani jirgin kamfanin Air Peace ya yi saukar gaggawa a jihar Legas.

An ruwaito cewa jirgin saman wanda ya taso daga Abuja zuwa Asaba, babban birnin jihar Delta ya yi saukar gaggawa a Legas sakamakon rahotannin samun matsalar fasaha a tsakiyar tafiya.

Kara karanta wannan

Jama’a sun ji haushin Sanusi II da sarki ya kawo shawarar gyara tattalin arziki

Air Peace.
Jirgin kamfanin Air Peace bayan ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama Hoto: Air Peace
Source: Getty Images

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an shirya jirgin ne da farko ya tashi daga Babban Birnin Tarayya (FCT) zuwa Asaba, Jihar Delta, amma daga baya aka karkatar da shi zuwa Legas.

Bayanan da muka samu sun njna cewa an karkatar da jirgin zuwa Legas ne bayan an samu rahoton matsala a ɗaya daga cikin na’urorinsa yayin tafiya.

Ana sa ran fasinjojin jirgin za su isa Asaba, babban birnin jihar Delta, amma karkatar da shi ya tilasta masa yin saukar da ba a shirya ba a Legas.

Ya zuwa yanzu, babu cikakken bayani kan irin matsalar fasaha da ta faru, halin da jirgin da fasinjojinsa suke ciki, ko kuma ko kamfanin jirgin ya shirya wani jirgin domin kai fasinjojin zuwa Asaba.

Za a kawo ƙarin bayani nan gaba...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262