Tozarta ni ake shirin yi shi yasa na yi murabus - Tsohon shuganan PDP na Imo
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Imo, Charles Ezekwem ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar PDP ne sakamakon hada kai da aka yi don tozarta shi bayan hukuncin kotun koli da ta kwace kujerar gwamnatin jihar daga hannun Emeka Ihedioha ta mika ta zuwa Hope Uzodinma.
Ezekwem wanda ya zanta da manema labarai a ranar Talata a garin Owerri, ya ce yin murabus dinsa ya biyo bayan burinsa ne na kare martabarsa a siyasance, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Ya ce “akwai hadin baki na tozarta ni bayan kwanaki biyu da kotun koli ta yanke hukunci. Sun nemi wani wanda zai maye gurbina amma sai yunkurin su ya fallasa. An fara mayar da ni kamar bako a gidan da ya kamata a ce ni ne shugaba. Sakataren jihar zai hada taro amma sai dai kawai ya turomin sakon gayyata bayan ni ne ya kamata in gayyaci wasu.”
DUBA WANNAN: 'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota
Ya kara da cewa, “Ban yi murabus ba saboda walwalata a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar. Na yi murabus ne don kare siyasa ta. Sun so su saukeni kafin cikar wa’adin mulkina a watan Augusta. A matsayina na jigo a jam’iyyar, na mika wasikar murabus dina zuwa shugaban jam’iyyar PDP na kasa baki daya.”
“Gerald Irona, mataimakin Gwamna Emeka Ihedioha ya sanar da mutane na, matukar suna biye da ni, toh babu mukamin da zasu samu a gwamnati. Bayan ni ne na dage don ganin nasarar gwamnan a jihar amma sai ake yi min kamar bako. Babu abinda suke yi wanda ban sani ba.” Ya kara da cewa.
“Ni na farfado da jam’iyyar a jihar Imo kuma ni na tabbatar da zaben fidda gwani na lumana a jihar Imo. Daga baya kuma sai aka fara ware ni daga al’amuran gwamnatin.” Ezekwem ya ce.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng