Bayan karbar kudin fansa, masu garkuwa da mutane sun kashe matar basarake

Bayan karbar kudin fansa, masu garkuwa da mutane sun kashe matar basarake

- Wasu masu garkuwa da mutane sun halaka matar babban basarake mai martaba Dr. Emmanuel Okoro Oha

- Sun je har gida ne inda suka yi gaba da Ugoeze Comfort Okoro bayan kwanaki kadan da suka yi bikin zagoyawar ranar aurensu karo na 50

- Kamar yadda kanin mai martabar ya sanar, an samu gawarta ne a Akobor Oguta bayan da iyalan suka biya kudin fansa

Ugoeze Comfort Okoro mata ce mai shekaru 76 ga basaraken Ihitoha Uratta da ke karamar hukumar Owerri ta Arewa a jihar. Ta rasu ne yayin da take hannun masu garkuwa da mutane bayan an basu kudin fansa, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

An ga gawar matar ne a kauyen Akabor da ke karamar hukumar Oguta a jihar a ranar Lahadi da ta gabata. An gano cewa masu garkuwa da mutanen sun sace matar ne a gaban mijinta da wasu hadimanta a ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu 2020. Lamarin ya faru kasa da wata daya bayan sunyi murnar cikarsu shekaru 50 da aure tare da mijinta.

Prince Paul Okoro, kanin mai gidan marigayiyar, Dr. Emmanuel Okoro Oha ne ya tabbatar da aukuwar lamarin da ya kwatanta da mai kunar rai. Ya ce an kashe ta ne bayan da iyalan suka biya kudin fansa.

Bayan karbar kudin fansa, masu garkuwa da mutane sun kashe matar basarake
Bayan karbar kudin fansa, masu garkuwa da mutane sun kashe matar basarake
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sirrin dukiya da daukakata ya dogara ne da yawan 'yan matan da nayi lalata dasu - Tsohon golan Najeriya

“A ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu 2020 ne wasu yara suka tsinkayi fadar suka sace matar mai martaba wajen karfe 8:30 na dare. Sun karba wayoyin jama’a har da ta mai martaba. Sun yi awon gaba da Ugoeze,” ya bayyana.

“Sai bayan kwanaki uku suka kira diyarta wacce ke auren dan majalisar tarayya, Ikenna Elezianya tare da bukatar kudin fansa. An gano gawarta a Akabor Oguta inda suka yasar da ita,” ya kara da cewa.

Daya daga cikin jami’an ‘yan sandar yankin ya tabbatar da cewa an kama wasu wadanda ake zarginsu da hannu cikin garkuwa da ita din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: