Wata jibgegiyar 'Kura' ta gudu daga gidan 'Zoo' a Imo, an kama ta bayan sa'a 6

Wata jibgegiyar 'Kura' ta gudu daga gidan 'Zoo' a Imo, an kama ta bayan sa'a 6

An kama wata kura da ta gudu daga gidan adana namun daji na jihar Imo a sa'o'in farko na yau Litinin. Kurar dai ta gudu ne daga Imo State Zoological Garden and Wildlife Park da ke Nekede a karamar hukumar Owerri ta yamma a jihar.

Kurar ta shiga hannun kwararu ne yau Litinin bayan tayi sa'o'i shida da tserewa daga ma'adanarta.

Babban manajan gidan namun dajin, Francis Abioye, ya tabbatar da guduwa tare da kara kama dabbar da aka yi a yau Litinin, kamar yadda jaridar the Nation ta ruwaito.

Kafin a kama dabbar, mazauna yankin sun fada tsananin rudani da tashin hankali wanda ya jawo rashin kwanciyar hankali garesu.

Amma kuma babban manajan da ya jagoranci kungiyar kwararrun da suka samu kamar Kurar, ya ce ba a samu wanda ta halaka ko ta raunata ba.

Wata jibgegiyar 'Kura' ta gudu daga gidan 'Zoo' a Imo, an kama ta bayan sa'a 6
Wata jibgegiyar 'Kura' ta gudu daga gidan 'Zoo' a Imo, an kama ta bayan sa'a 6
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zuwa da mata zauren majalisa: Mahaifina ya mutu ya bar 'ya'ya fiye da 40 - Hon. Alasan Doguwa

Ya ce sun dau sa'o'i shida suna nema tare da dabarunsu na kwararru kafin su damketa.

A yayin bayanin yadda Kurar ta gudu, Abioye ya ce dabbar ta haka rami ne ta karkashin kasa wanda ta samu ta zirare ta cikin shi daga kejinta.

Ya ce dabbar na fita kuwa ta shiga gari abunta bayan ta tsallake wani bango da ke cikin gidan Zoo din. Ya zargi cewa matasan yankin ne suka lalata bangon tun a 2019.

"Zan iya tabbatar muku da cewa wata katuwar Kura ta gudu daga kejinta da safen nan ta karkashin kasa amma kwararru sun kama ta da safen nan. Dabbar ta tsere daga farfajiyar gidan ne ta wani bango da matasa suka lalata," ya ce.

Abioye ya shawarci jama'ar yankin da su koma aiyukansu tare da walwalarsu kamar da don komai ya lafa kuma dabbar na killace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng