Siyasa na Ɗaukar Zafi, Ƴan Daba Sun Farmaki Ɗan Takarar Majalisa, an Rasa Rai

Siyasa na Ɗaukar Zafi, Ƴan Daba Sun Farmaki Ɗan Takarar Majalisa, an Rasa Rai

  • Rundunar ’yan sandan Ebonyi ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, yayin da wasu uku suka jikkata bayan wasu ’yan daba sun kai hari ayarin ɗan takarar NDC
  • Ɗan takarar majalisar dokokin jihar, Rollins Offia-Nwali, ya ce maharan sun ƙona motarsa kirar Toyota Hilux, amma shi da tawagarsa sun tsira ba tare da rauni ba
  • Offia-Nwali ya yi ta’aziyya ga waɗanda harin ya shafa, tare da gargaɗin matasa kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen cimma muradunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Rundunar ’yan sandan jihar Ebonyi ta ce mutum ɗaya ya mutu, yayin da wasu uku suka jikkata bayan an kai hari ayarin Rollins Offia-Nwali, ɗan takarar jam’iyyar NDC.

Rahotanni sun bayyana cewa Joshua Ukandu, kakakin rundunar ’yan sandan Ebonyi, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin Alhamis.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun farmaki ayarin ɗan takarar jam'iyyar su Kwankwaso, an kashe mutum 1

An kai hari kan dan takarar majalisa na NDC
Sufeta-janar na yan sanda a Najeriya, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Yadda yan Daba suka farmaki ɗan takara

Ya ce harin ya faru ne a garin Amaezekwe da ke ƙaramar hukumar Ezza ta Kudu a jihar Ebonyi, cewar rahoton TheCable.

Ukandu ya bayyana cewa rundunar ta samu kiran gaggawa game da rikici a yankin, inda nan take ta tura jami’anta zuwa wurin da lamarin ya faru.

Ya ce:

“Lokacin da jami’an suka isa wurin, sun tarar da mutane huɗu da raunukan harbin bindiga, da kuma wata mota da aka ƙona.
"An tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa a asibiti, yayin da sauran ukun ke samun kulawar likitoci.”
Yan daba sun farmaki ɗan NDC
Taswirar jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da dan takarar majalisar ya ce

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ɗan takarar jam’iyyar NDC ya ce wasu da ake zargin ’yan daba ne masu alaƙa da siyasa sun kai hari ayarinsa.

Offia-Nwali ya ce maharan sun cinna wa motarsa kirar Toyota Hilux wuta a yayin harin wanda ya tayar wa wadanda ke kusa da wurin hankali matuka.

Kara karanta wannan

Makinde ya faɗi dalilin ƙalubakantar Tinubu duk da sun fito daga yanki ɗaya

Ya ƙara da cewa shi da sauran mutanen da ke tare da shi sun tsira ba tare da sun samu wani rauni ba inda ya yi godiya ga Ubangiji, cewar Punch.

Ɗan takarar ya nuna alhini ga waɗanda harin ya shafa, tare da kira ga matasan jihar da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen cimma muradunsu.

Ya ce:

“Babu wani burin siyasa da ya kai darajar rayuwar matashi.”

An kai farmaki kan dan takarar gwamna

A wani labarin mai kama da wannan, PDP reshen jihar Cross River ta zargi wasu ‘yan daba da kai hari kan ayarin dan takararta na gwamna, Sir Arthur Javis-Archibong, a Kalaba ta Kudu.

Javis-Archibong ya ce an kai wa ayarinsa hari a wurare biyu, inda mutane uku suka jikkata tare da lalata motoci wanda ya ce jawo masa asara mai yawa.

Jam’iyyar ta ce magoya bayanta sun kaurace wa ramuwar gayya, yayin da ‘yan sanda ke tabbatar da rahotannin harbe-harbe da jikkatawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.