Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari
Ana rikici tsakanin wasu Kabilu a Yankin Mokwa da Katcha a Neja. Rigimar wannan Kabilu ta ci mutane a Jihar Neja inda yanzu aka nemi Shugaban kasa ya sa baki a cikin rikicin tun kafin abu ya cabe.
Manyan Manoman jihar Katsina sai san barka a bana inda su ka samu amfani sosai na shinkafa. Yanzu shinkafa ta isa kasuwanni bayan damina ta yi kyau kuma an tserewa harkar masara.
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya gargadi yan ta’adda a jihar da su shirya fuskantar mummunan mataki daga gwamnatin idan har basu shiryu ba. Masari ya fadi hakan ne yayinda yake jawabi a wani tsaron tsaro tare da sarakuna.
Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya umarci sakataren gwamnatin jahar Katsina, Mustapha Inuwa ya shirya zaman tattaunawa tsakanin gwamnati, shuwagabannin hukumomin tsaro da yan bindiga domin tattauna batun sulhu.
Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya gayyaci shuwagabannin al’ummar Fulani dake zaune a kananan hukumomi guda 9 na jahar Katsina domin tattauna hanyar kawo karshen matsalolin tsaro a jahar.
Ruwan dare ya rusa gidaje fiye da 100 a Daura da ke Jihar Katsina. Gidajen mutane sama da 100 sun ruguje a dalilin wannan ruwa mai karfi da aka fara tun safiyar Ranar Lahadi inda ya yi ta kwarara har dare.
Wasu yan bautar kasa biyu a jihar Katsina, a ranar Lahadi, 17 ga watan Agusta sun mutu a wani mummunan hatsarin mota, da ya afku a kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Kankara da ke jihar.
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana farin ciki a kan kyakkyawar kulawa da kuma ci gaba na aminci da al'ummar jihar Katsina ke samu tsawon shekaru hudu a karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari.
Gwamnatin jihar Katsina bisa jagorancin gwamna Aminu Bello Masari, ta kammala ginin wannan babbar hanya a kan zunzurutun kudi na naira biliyan 3.3 da manufar saukaka wa manoma wajen fidda amfanin gonakinsu zuwa wajen jihar.
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari
Samu kari