Kan iyakar kasa ya hada mutanen Katcha da Kpata-katcha fada
Mutanen Kpata-katcha da ke zaune akaramar hukumar Mokwa da ke jihar Neja, sun yi kira ga shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya shiga cikin rikicin iyakarsu da mutanen Katcha.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mutanen wannan shiyya sun dauki rikicinsu zuwa ga shugaban kasa ganin cewa ana cigaba da rasa rayukan Bayin Allah domin abin ya ki ci ya ki cinyewa.
Rahotanni sun bayyana cewa an dade ana wannan rikici wanda yayi sanadiyyar rashin mutane. Wannan ya sa gwamnatin jihar Neja ta kafa kwamiti na musamman a baya domin ya binciki a lamarin.
Mutanen yankin na Mokwa da kuma Kacha sun koka da cewa shekara guda rikicin baya ya faru, jama’a sun gaza komawa gidajensu saboda nawan da gwamnatin Neja ta ke yi wajen sasanta rigimar.
KU KARANTA: Rundunar yan sandan jihar Neja sun kama wanda ta saida yaro
Dr. Saganuwan Alhaji Saganuwan ya fadawa ‘yan jarida cewa idan har gwamnati ba ta kawo karshen wannan rigima ba, jihar Neja na iya burmawa cikin babban hadari nan gaba kadan.
Dattijon ya jawo hankalin gwamnan jihar cewa ana masa zagon kasa wajen shirin da ya ke yi na kawo zaman lafiya a yankin. Alhaji Saganuwan yace ya kamata a ba sha’anin tsaro muhimmanci.
Shekara guda kenan da rikici ya barke a shiyyar jihar kuma har yanzu da-dama su na tsare bas u koma gida ba. Mutanen na Mokwa sun a ganin kwamitin da aka kafa ba tayi aikin da ya dace ba.
A karshe yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kokari wajen ganin mutanen da su ka bar matsuguninsu sun koma gida domin cigaba da kasuwanci da harkokin yau da kullum.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng