"Ka da Ku": Shawarar Sanusi II ga Masu Son Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote

"Ka da Ku": Shawarar Sanusi II ga Masu Son Sayen Hannun Jarin Matatar Dangote

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bayar da shawara ga mutanen da ke son saka hannun jarinsu a matatar Dangoge
  • Ya bukaci ’yan Kano su zuba kuɗin da za su iya ajiyewa na dogon lokaci, yana ba da misalin N10,000, N20,000 ko N30,000
  • Sanusi ya ce masu hannun jari ne ke mallakar kamfanin tare da samun ribarsa, ba tare da la’akari da inda aka gina matatar man ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana kan sayen hannun jari a matatar Dangote.

Sanusi II ya shawarci masu shirin saka jari da kada su yi amfani da muhimman kuɗaɗen tafiyar da rayuwa, kamar kuɗin makarantar ’ya’yansu ko gidajen da suke zaune, wajen sayen hannun jari.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya tuna zamansa a CBN, ya fadi babbar nadamar da ya yi

Sanusi II ya bayar da shawara
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Twitter

Sarkin ya yi wannan shawarar ne ranar Alhamis, 17 ga watan Satumban 2026 yayin wani taron wayar da kan masu zuba jari kan sayen hannun jarin matatar Dangote da aka gudanar a Kano, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Ya nemi a sanya kuɗin da za a yya ajiyewa

Sanusi II ya bukaci mazauna Kano su zuba kuɗin da za su iya warewa na dogon lokaci ba tare da hakan ya jefa su cikin matsalar kuɗi ba.

Ya ba da shawarar a fara da kuɗaɗe masu sauƙi, kamar N10,000, N20,000 ko N30,000, maimakon neman samun riba cikin gaggawa ta hanyar saye da sayar da hannun jari cikin ɗan lokaci.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta fito da tsari, duk wanda ya sayi hannun jari zai iya samun kyauta mai gwaɓi

“Kar ku ɗauki kuɗin makarantar ’ya’yanku ku saka a hannun jari. Kada ku sayar da gidan da kuke zaune ku saka kuɗin a hannun jari."
“Amma abin da za ku iya warewa, N10,000, N20,000 ko N30,000, ku ware shi na wani lokaci. Idan kuka duba muhimman abubuwan tattalin arzikin ƙasar, a hankali za ku ga wannan jari na iya ƙaruwa,” in ji shi.

“Ina son mutanena su zama masu kamfanin”

Sanusi II ya ce yana magana ne a matsayinsa na Sarkin Kano, yana mai bayyana burinsa na ganin mutanen Kano sun mallaki wani kaso na kamfanin.

“Ba na son a bar mu a baya a kasuwar hada-hadar hannun jari. Ba na son a bar mu a baya wajen shigar da jama’a cikin harkokin kuɗi. Wannan shi ne lokacin kuma wannan ita ce damar.” in ji shi.

Ya gargadi masu neman riba cikin gaggawa

Sarkin ya kuma shawarci masu zuba jari da su rungumi tsarin saka kuɗi na dogon lokaci, maimakon sayen hannun jari da nufin sayar da shi gobe domin samun riba mai yawa.

Kara karanta wannan

Cikin awa 1 da bude saida hannun jari, Matatar Dangote ta samu Dala miliyan 7

Ya ce bai kamata mutum ya sayi hannun jari 5,000 da nufin sayar da su washegari domin ninka kuɗinsa ba.

Sanusi ya ce ya fi dacewa mutum ya saka kuɗin da yake da shi, ya bar shi na wani lokaci sannan ya bibiyi yadda jarinsa ke ƙaruwa.

Ya ce mutum zai iya mamakin irin darajar da N10,000 ko N100,000 da ya saka a yau za su iya kaiwa bayan shekaru biyar.

Sanusi II ya bayar da shawara kan sayen hannun jari
Muhammadu Sanusi II zaune yana karatu Hoto: Sanusi II Dynasty
Source: Facebook

Kuskuren Sanusi II lokacin da yake CBN

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana kuskuren da ya yi lokacin da yake shugabantar CBN.

Sanusi II ya ce yana nadamar jinkirta shigar kamfanonin sadarwa cikin harkar samar da ayyukan kuɗi a lokacin da yake gwamnan CBN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng