Mabiyan Sheikh Lukuwa Sun Kawo Cikas a Matakin da Aka Dauka kan Taba Iyayen Annabi SAW
- Mabiyan malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Lukuwa, sun yi watsi da kwamitin mutum 14 da Gwamnatin Jihar Sokoto ta kafa domin bincike
- Sun yi zargin cewa wasu mambobin kwamitin sun taɓa samun saɓani da Sheikh Lukuwa kan wasu batutuwan addini
- Mai magana da yawun Lukuwa ya ce ya kamata a warware saɓanin addini ta hanyar ilimi da tattaunawa ba da ƙarfi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Mabiyan Sheikh Musa Lukuwa, sun ƙi amincewa da kwamitin mutum 14 da Gwamnatin Jihar Sokoto ta kafa domin binciken yanayin da ya kai ga harin da aka kai wa malamin a masallacinsa da ke Mabera.
Sun yi zargin cewa wasu daga cikin mambobin kwamitin sun taɓa samun saɓani da Lukuwa kan batutuwan addini, don haka za su iya nuna son kai wajen gudanar da binciken.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun mamaye gidan kwamishina, sun bude wuta ba tare da nuna tausayi ba

Source: Facebook
An kafa kwamitin bincike a Sokoto
Daily Trust ta rahoto cewa an kai wa Lukuwa hari ne jim kaɗan bayan ya jagoranci sallar Juma’a a masallacinsa da ke Mabera, Sokoto, ranar Juma’ar da ta gabata.
Bayan faruwar lamarin, gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe masallacin tare da kafa kwamitin malaman addinin Musulunci domin duba batutuwan addini da suka shafi rikicin.
Kwamitin, wanda Sarkin Malamai, Malam Yahya Na Malam Boyi, ke jagoranta, an ba shi kwanaki 14 domin duba matsayin Shari’a kan batutuwan da Lukuwa ya gabatar da kuma bai wa gwamnati shawarwari.
Mabiyan Lukuwa sun fi fatali da kwamitin
Da yake magana da manema labarai yau Alhamis, kakakin Lukuwa kuma babban ɗalibinsa, Sheikh Murtala Assada, ya ce mabiyan malamin ba su gamsu da yadda aka tsara kwamitin ba.
Ya yi zargin cewa wasu daga cikin waɗanda aka naɗa sun dade suna adawa fa Sheikh Lukuwa kan matsayinsa game da ganin jinjirin wata da wani Hadisi da ya ambata yayin karatunsa, wanda wasu mutane suka fassara shi a matsayin raini ga iyayen Annabi Muhammad (SAW).
Ya ce ya kamata a mika batun ga malaman addini domin gudanar da bincike na ilimi maimakon a mayar da shi rikici.

Source: Facebook
Abin da mabiyan Lukuwa suke bukata
Sheikh Mustala Assada ya ce:
“Idan abin da suke so shi ne adalci, ya kamata su gayyaci malaman addini sannan su gayyaci Sheikh Lukuwa domin su zauna tare su tattauna batun.
“Wannan batu ne na ilimi. Ya kamata su tambaye shi dalilin da ya sa ya ambaci Hadisin, inda ya samo shi da kuma waɗanne malamai ne suka fassara shi kamar yadda ya yi.
“Idan ya nuna musu inda Hadisin yake kuma ya bayyana malaman da suka fassara shi haka, to ya kamata a kawo ƙarshen batun a nan. Amma idan bai iya gabatar da hujjoji ba, to doka ta yi aikinta."
Sunayen mambobin kwamitin da aka kafa
Kun ji cewa gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ya kafa kwamitin mutum 14 domin bincike kan kalaman da ake dangantawa da Sheikh Musa Lukuwa da ake zargin sun taba iyayen Annabi Muhammad SAW.
Mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa, ne ya bayyana kafa kwamitin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya jero sunayen duka yan kwamitin.
Asali: Legit.ng
