Allah raya jahar Katsina: Gwamnoni 10 da suka mulki jahar Katsina tun 1987

Allah raya jahar Katsina: Gwamnoni 10 da suka mulki jahar Katsina tun 1987

A ranar 23 ga watan Satumba na shekarar 1987 ne gwamnatin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta kirkiro jahar Katsina daga cikin jahar Kaduna, wanda hakan yasa a yanzu Katsina ta cika shekaru 32 da kirkira.

Legit.ng ta binciko muku jerin dukkanin gwamnonin da suka taba mulkan jahar tun daga 1987. Daga cikin gwamnanonin da suka mulki jahar Katsina akwai Sojoji guda 7, sai kuma wadanda suka yi mulkin farar hula guda 3, duba jerin shuwagabannin da suka mulkin Katsina kamar haka;

KU KARANTA: Murnar cikar Katsina shekaru 32: Jama’an Daura sun nemi a basu takarar gwamna

- Abdullahi Sarki Mukhtar daga 1987 zuwa 1988 mulkin Soja

- Lawrence Onoja daga 1988 zuwa 1989, mulkin Soja

- John Madaki daga 1989 zuwa 1992, mulkin Soja

- Saidu Barda daga 1992 zuwa 1993, jam’iyyar NRC

- Emmanuel Acholonu daga 1993 zuwa 1996, mulkin Soja

- Samaila Bature Chamah daga 1996 zuwa 1998, mulkin Soja

- Joseph Akaageger daga 1998 zuwa 1999, mulkin Soja

- Umaru Musa Yar’adu daga 1999 zuwa 2007, jam’iyyar PDP

- Ibrahim Shema daga 2007 zuwa 2015, jam’iyyar PDP

- Aminu Bello Masari, daga 2015 zuwa yanzu, jam’iyyar APC

Sai dai a yayin da ake murnar cikar jahar Katsina shekaru 32, al’ummar yankin masarautar Daura sun koka game da wariya da ake nuna musu a harkar siyasar jahar, don haka suka nemi a basu takarar shugabancin gwamnatin jahar a zaben shekarar 2023.

Cikin wata sanarwa da Ahmed Ahidjo Wali da Sada Bawa suka fitar a cikin wata talla sun bayyana cewa tsawon shekaru 32 ana nuna ma yankin Daura wariya tare da mayar dasu saniyar ware a siyasar jahar duk kuwa da cewa sun bayar da gudunmuwa ga cigaban jahar tsawon shekarun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel