Sulhu da 'yan bindiga: Tawagar gwamnonin arewa hudu ta dira a jamhuriyar Nijar

Sulhu da 'yan bindiga: Tawagar gwamnonin arewa hudu ta dira a jamhuriyar Nijar

A kokarinsa na kawo karshen aiyukan 'yan bindigar da suka addabi sassan Katsina da kisan jama'a ba dare ba rana, gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya fara tattauna wa da takwaransa na jihar Maradi a jamhuriyar Nijar, Alhaji Zakari Umaru.

Jihar Maradi ta jamhuriyar Nijar ta yi iyaka da Najeriya ta jihar Katsina da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Tawagar da masari ya nada karkashin sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dakta Mustafa Mohammed Inuwa, ta dira a jamhuriyar Nijar tare da wasu gwamnoni uku; Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara, Aminu Waziri Tambuwa na jihar Sokoto da Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Sun tattauna a kan magance aiyukan 'yan bindigar a tsakanin jihohin na arewacin Najeriya da makwabtan garuruwan jamhuriyar Nijar.

Ziyarar da tawagar ta kai jamhuriyar Nijar na zuwa ne a daidai lokacin da gwamna Masari ya fara tattauna wa domin yin sulhu da 'yan bindigar da suka hana kananan hukumomi takwas daga cikin 34 na jihar Katsina zaman lafiya.

'Yan bindigar sun kashe mutane da dama tare da lalata dukiya mai yawa a hare-haren da suke kai wa a sassan jihar Katsina.

DUBA WANNAN: 'Yan bindigar Katsina: Su waye su?

Hare-haren 'yan bindigar sun fi tsanani a kananan hukumomin Dandume, Faskari, Kankara, Danmusa, Safana, Batsari da Jibiya. Dukkan kananan hukumomin sun yi iyaka da surkukin jejin 'Rugu'.

Bisa la'akari da irin nasarar da sulhu da 'yan bidigar a jihar Katsina ke samu, gwamna Masari ya bayyana karfin gwuiwarsa a kan cewa tattaunawar da aka fara yi a Maradi zata kawo karshen duk wani kalubale da barzanar tsaro da jiharsa da makwabatan jihohi ke fuskanta.

Rahotannin jami'an tsaro sun tabbatar da cewa 'yan bindigar na safarar makamai ta iyakar jihohin arewacin Najeriya hudu da Maradi, kuma ta nan ne suke shiga ko fita daga Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel