Daura: Gidajen mutane da-dama sun ruguje dalilin ruwa mai karfi

Daura: Gidajen mutane da-dama sun ruguje dalilin ruwa mai karfi

- Daruruwan gidaje sun ruguje a sanadiyyar ruwan sama mai karfi a Daura

- Ruwan da a ka yi ci gidajen mutane da-dama a Mahaifar Shugaban kasar

- An fara ruwan ne tun safiyar Ranar Lahadi inda a ka dade ya na kwarara

A yau Litinin 26 ga Watan Agusta, 2019, labari ya ke zuwa mana cewa wani ruwa da ya barke kamar da bakin kwarya a jihar Katsina ya ci gidajen jama’a. Wannan abu ya faru ne a Garin Daura.

Ruwan da a ke sheka a jiya Ranar Lahadi ya rusa gidajen mutane ne a cikin Garin na Daura da ke Arewacin jihar Katsina. Wannan ruwa mai karfi ya yi wa mutane fiye da dari illa a Garin jiya.

Kamar yadda mu ka samu labari, an fara ruwan ne tun jiya da sassafe, wanda a ka dauki dogon lokaci ya na sauka. A dalilin haka a ka samu ambaliyar da ta rusa gidaje a Unguwanni da dama.

KU KARANTA: Amarya da Ango sun mutu bayan an gama daurin aure

Daga cikin unguwannin da wannan musiba ta aukawa a babban Garin na jihar Katsina akwai Kalgo, da Rahmawa. Haka zalika ruwan saman ya yi gyara a Bayan Motel da Lungun Kofar Baru.

Bayan nan, gidaje da dama sun rushe a cikin Unguwanan na Sarkin Yara wanda a ke kira Unguwan Kaura. A nan ne inda shugaban kasa Buhari ya ke zabe idan ya je hutu a Kauyen na sa.

Wani Bawan Allah da ruwan markan ya sauka a kansu, ya bayyana cewa a Unguwar Kalgo kurum, sama da gidaje 50 su ka rushe. Ya ce: “Tun karfe 7:00 na safiyar Lahadi a ka fara ruwan saman.”

A lokacin da wannan mutumi ya ke magana da ‘yan jarida, ya bayyana masu cewa har zuwa wannan lokaci a na cigaba da sheka ruwa. Mazaunin Garin ya ce gidaje kusan 100 sun rushe.

Mutanen Yankin na Daura sun nemi hukuma ta yi maza ta kawo masu dauki. An dai yi dace babu wanda ya samu rauni ko ya mutu a dalilin wannan ruwan sama mai nauyi mai tsawo da a ka yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel