Gwamna Masari ya yi wa yan bindiga gargadi da kakkausar murya

Gwamna Masari ya yi wa yan bindiga gargadi da kakkausar murya

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya gargadi yan ta’adda a jihar da su shirya fuskantar mummunan mataki daga gwamnatin idan har basu shiryu ba.

Masari ya fadi hakan ne yayinda yake jawabi a wani tsaron tsaro tare da sarakunan gargajiya, shugabannin makiyaya da kuma hukumomin tsaro a jihar a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta.

Yace ba za a yarda da kashe-kashen da ake yi ba sannan yayi kira ga iyaye akan su sanya idanu sosai akan yaransu domin hana su shiga kungiyar yan bindiga da sauran kungiyoyin yan ta’adda.

Ya kuma ba al’umman jihar tabbacin cewa gwamnati zata yi aiki da duk wata kungiya da ta shirya zaman lafiya, don tabbatar da ganin zaman lafiya ya dawo a garuruwan kakkara na jihar.

Da yake jawabi, Abdulmumini Kabir, sarkin Katsina, yayi kira ga ayi gaggawan dakatar da zubar da jini.

KU KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sandan jihar Anambra ta kama barayin motoci da wayoyi har 150

Ya yi kira ga garuruwan da ke karkashinsa da su ci gaba da zama lafiya da junansu, inda ya bayyana halin da ake ciki na kashe-kashe a jihar a matsayin abun kaico.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel