Zan saka kafar wando daya da yan bindiga da masu garkuwa – Gwamna Masari

Zan saka kafar wando daya da yan bindiga da masu garkuwa – Gwamna Masari

Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya gayyaci shuwagabannin al’ummar Fulani dake zaune a kananan hukumomi guda 9 na jahar Katsina domin tattauna hanyar kawo karshen matsalolin tsaro a jahar.

Gwamnan ya yi wannan zaman tattaunawa da Fulani ne sakatariyar gwamnatin jahar a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta inda aka yi zube ban kwaryata tsakanin bangarorin biyu da nufin shawo kan matsalar tsaro da ake fama da ita a jahar.

KU KARANTA: Sabuwar shekarar Musulunci 1441: Jahar Osun ta bayar da hutun aiki na kwana 1

Masari ya bayyana ma shuwagabannin Fulani cewa ya gaji da wannan matsala, don haka daga yanzu zai sanya kafar wando daya da duk wasu yan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka fitinin jahar Katsina.

Gwamnan ya cigaba da cewa: “Muna sa ran wannan tattaunawa zai kawo karshen kashe kashe da sace sacen mutane da dukiyoyinsu ba kawai a iya kananan hukumomi 9 da abin ya shafa ba, hatta sauran kananan hukumomin jahar gaba daya. Aikin tsaro ba aikin gwamna bane kadai, aiki ne na kowa da kowa.”

A jawabinsa, mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Kabir Usman ya yi kira jama’a dasu hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalar tsaro a jahar, tare da kawo karshensa gaba daya, don haka ya nemi majalisar dokokin jahar ta gaggauta kammala aiki kan dokar data tanadi hukuncin kisa a kan barayin shanu da masu garkuwa da mutane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng