Buhari ya kaddamar da sabon titi na N3.3bn a Katsina

Buhari ya kaddamar da sabon titi na N3.3bn a Katsina

A ranar Laraba 14 ga watan Agusta, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya jagoranci bude wani sabon katafaren aiki na ginin titi mai tsawon mita dubu 33 da gwamnatin jihar Katsina ta kammala.

Gwamnatin jihar Katsina bisa jagorancin gwamna Aminu Bello Masari, ta kammala ginin wannan babbar hanya a kan zunzurutun kudi na naira biliyan 3.3 da manufar saukaka wa manoma wajen fidda amfanin gonakinsu zuwa wajen jihar.

Babbar hanyar da shiga cikin yankunan Shinkafi, Yandaki, Gafia, Abdallawa da kuma Dankaba, ta ratsa ta cikin shiyoyi 15 dake cikin birnin Dikko da kuma karamar hukumar Kaita a jihar Katsina.

Mutane da dama sun yi tururuwa ta shaidawa a yayin bude wannan katafaren aiki da aka fara gudanar da shi tun a watan Oktoba na shekarar 2017. An kuma kammala shi a watan Afirlun 2019 da ya gabata.

Da yake zayyana jawabansa na farin ciki, shugaban kasa Buhari ya yabawa kwazon gwamnatin jihar Katsina da ta kasance mahaifarsa, inda ya ce hobbasan da gwamnatin ke yi ya yi daidai da akidarsa ta kawo mangarcin sauyi a kasar.

KARANTA KUMA: Najeriya na gab da tsarkaka daga cutar shan inna

Baya ga kawo sauki na sufuri, shugaban kasar ya ce babbar hanyar za ta taka muhimmiyar rawar gani wajen inganta jin dadin al'ummar yankunan da ta ratsa cikin su.

Gwamna Masari ya ce, ba ya ga wannan aiki, a gobe kuma da ta kasance ranar Alhamis, shugaban kasa Buhari zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatinsa ta kammala bayan cin gajiyarsu a hannun tsohon gwamnan jihar, Alhaji Shehu Shema.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng