Tura Ta Kai Bango: Dattawa daga Arewa Sun Aika Sako ga Tinubu bayan Fetur Ya Kai N1500

Tura Ta Kai Bango: Dattawa daga Arewa Sun Aika Sako ga Tinubu bayan Fetur Ya Kai N1500

  • NOSCEF ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta janye sabon ƙarin farashin man fetur saboda wuyar da jefa ’yan Najeriya
  • Ƙungiyar ta ce hauhawar tsadar rayuwa, yunwa, rashin aikin yi, rashin tsaro da tsadar sufuri na ƙara jefa iyalai cikin matsin tattalin arziki
  • NOSCEF ta bukaci gwamnati ta mayar da hankali kan rage tsadar rayuwa, samar da ayyukan yi, tsaro da gyaran muhimman ababen more rayuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ƙungiyar dattawan Kiristocin Arewacin Najeriya, (NOSCEF), ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta janye sabon ƙarin farashin man fetur.

Ƙungiyar ta ce ƙarin farashin man fetur zai ƙara tsananta halin matsin tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta a faɗin ƙasar.

An bukaci Tinubu ya janye karin farashin mai
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tarayyar Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Channels tv ta ce hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Elder Sunday Oibe, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Farashin litar fetur na iya haura N5000 bayan zaben 2027, an gano dalili

NOSCEF ta bayyana damuwarta kan hauhawar tsadar rayuwa da yunwa da rashin tsaro da rashin aikin yi.

NOSCEF ta yi magana kan tsadar rayuwa

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan ƙarin kuɗin sufuri da raguwar ƙarfin da iyalai ke da shi na sayen abubuwan da suke buƙata.

NOSCEF ta tambayi dalilin ƙara farashin man fetur a daidai lokacin da miliyoyin ’yan Najeriya ke fama da matsalar biyan buƙatun yau da kullum.

A cewarta, idan gwamnatin tarayya na buƙatar ƙarin kuɗaɗe domin gudanar da shirye-shiryenta da kuma cika wasu wajibcinta, ya kamata ta nemi hanyoyin samun kuɗin da za su dore ba tare da ƙara wa talakawa nauyi ba.

Wace shawara kungiyar ta ba Tinubu?

NOSCEF ta bukaci Shugaba Tinubu ya yi amfani da sauran lokacin mulkinsa wajen aiwatar da matakan da za su rage wa ’yan Najeriya wahala.

Ƙungiyar ta ce ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan dawo da ƙarfin saye, samar da ayyukan yi, ƙarfafa tsaro da kuma magance matsalar lalacewar muhimman ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Musulmai sun ɗauki mataki mai tsauri da aka gano yan bindiga na shirin kai hari masallatai

Ta amince cewa gwamnatin Tinubu ta yi hubbasa a fannoni daban-daban, amma ta ce ci gaba da fuskantar matsaloli a ƙasar na nuna cewa akwai sauran abubuwa da ya kamata a yi.

“Mu na cikin jama’a”

Ƙungiyar ta kuma roƙi Shugaban ƙasar da ya kasance mai fahimtar halin da talakawan Najeriya ke ciki.

NOSCEF ta ce mambobinta suna rayuwa da kuma gudanar da ayyukansu a tsakanin jama’a, don haka suna fuskantar ƙalubalen da al’ummomi ke fama da su kai tsaye.

Ta buƙaci gwamnatin tarayya ta sake duba sabon ƙarin farashin man fetur tare da janye shi, rage tsadar rayuwa da samar da hanyoyin samun ayyukan yi masu amfani ga matasa.

Dattawa sun aika sako ga Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

An yi hasashen kuri'un da Tinubu zai samu

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar sakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya hango kuri'un da mai girma Bola Tinubu zai samu a 2027.

Abdulmumin Jibrin ya yi hasashen cewa Shugaba Tinubu zai samu akalla kashi 65 na jimillar ƙuri’un da za a kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng