Babbar Magana: An Nemi a Tura Wasu Malaman Musulunci zuwa Wurin Yan Bindiga

Babbar Magana: An Nemi a Tura Wasu Malaman Musulunci zuwa Wurin Yan Bindiga

  • Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya sake kawo shawarar yadda za a magance matsalar yan bindiga a Najeriya
  • Gumi ya ce tura amintattun malaman Musulunci zuwa dazuzzuka domin ilmantar da ’yan bindiga na iya taimakawa wajen kawo ƙarshen ayyukansu a Arewa
  • Babban malaminnya sake jaddada goyon bayansa ga hanyoyin ruwan sanyi wajen magance matsalar ’yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana yadda amintattun malaman Musulunci za su iya taimaka wa wajen kawo karshen yan bindiga.

Ya ce malamai za su iya zuwa dazuzzuka domin tattaunawa da ’yan bindiga da kuma ilmantar da su kan addini, wanda hakan zai iya taimakawa wajen kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Olu Jacobs: Abubuwan sani game da fitaccen jarumin fim da Allah ya yi wa rasuwa

Ahmad Gumi.
Babban malamin addinin Musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi Hoto: Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Gumi ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook ranar Laraba, inda ya sake jaddada goyon bayansa ga bin hanyoyin ruwan sanyi maimakon daukar matakin soja.

Ya ce malaman za su iya haduwa ƙungiyoyin yan ta'adda, su koya musu muhimmancin rayuwar ɗan Adam da kuma yadda Musulunci ya haramta kisa da zalunci, tare da ƙarfafa su da su kaucewa tashin hankali

Gumi ya ce malamai za su iya taimakawa

Malam Gumi ya ce idan da an tura ƙarin amintattun malaman Musulunci cikin tsari zuwa dazuzzuka domin tattaunawa da ƙungiyoyin yan bindiga, da yanzu abubuwa sun fara dawowa daidai

“Tun daga 2021, yanzu kusan shekaru shida kenan da muka fara wa’azi ga ’yan bindiga, babu wanda zai iya hasaso abin da za a iya cimma ba idan da an tura malaman Musulunci cikin tsari domin tattaunawa da ’yan bindiga a sassan Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Farashin litar fetur na iya haura N5000 bayan zaben 2027, an gano dalili

"Za su koya musu muhimmancin rayuwar ɗan Adam, cewa dukiyar mutane abu ce mai tsarki da ba za a taɓa ba, da kuma haramcin kisa da zalunci a Musulunci,” in ji Gumi.

Sheikh Gumi ya bukaci a bi hanyar sulhu

Malamin ya kuma ce tattaunawa ba tare da tashin hankali ba na iya rage buƙatar kai hare-haren soji ta hanyar magance wasu matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da ke haddasa rikicin.

Gumi.
Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi Hoto: Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Ahmad Gumi ya ce rashin samun isasshen ilimi, talauci da kuma sakaci sun shafi da yawa daga cikin ’yan bindigar, lamarin da ya ce ya taimaka wajen yaɗuwar matsalar.

“Mutane kalilan ne suke fahimtar cewa da yawa daga cikin waɗannan ’yan bindigar sun shiga wannan halin ne sakamakon jahilci, talauci da kuma sakacin al’umma,” in ji shi.

Sheikh Gumi ya kare Sanata Shehu Buba

A wani labarin, kun ji cewa Shiekh Ahmad Abubaar Mahmud Gumi ya tsoma baki kan zargin Sanata Shehu Buba daga jihar Bauchi kan alaka da ta'addanci.

Malamin ya bayyana irin gudunmawar da sanatan ya bayar wurin tabbatar da kawo karshen matsalolin tsaro da ke damun al'umma.

Sheikh Gumi ya ce bambancin ra’ayin siyasa halas ne, amma da gangan ɓata sunan mutumin da ya bayar da gudunmawa wajen yaƙi da rashin tsaro rashin adalci ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262