An Samu Matsala: Mutane Fiye da 30 Sun Mutu a Ofishin Hukumar NSCDC Ta Najeriya
- Mutane 33 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun mutu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula da Kare Muhalli ta Najeriya (NSCDC)
- An kama mutanen ne tare da wasu mutane bakwai a wani samame da aka kai domin dakile ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba
- Rahotanni sun ce an tsinci gawarwakin mutanen 33 da sanyin safiyar Alhamis, inda aka ga kumfa na fitowa daga bakunansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Mutane 33 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun mutu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula da Kare Muhalli ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Neja.
An ce Mutanen da suka mutu na daga cikin mutane 40 da aka tsare a sashen maza na ɗakin tsarewar NSCDC bayan kama su yayin wani samame kan ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a jihar.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya yi maganar sayen hannun jari a matatar Dangote, ya ba 'yan Najeriya shawara

Source: UGC
Leadership ta ruwaito cewa an tsinci gawarwakin mutane 33 da sanyin safiyar yau Alhamis, inda rahotanni suka ce kumfa na fitowa daga bakunansu.
An tsinci gawarwakin mutane 33
Kwamandan NSCDC na Jihar Neja ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kama waɗanda ake zargin ne a wani wurin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce hukumar ta gudanar da wani samame a ranakun 15 da 16 ga Satumba 2026, a wani sabon yunƙuri na dakile ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a jihar.
A cewarsa, samamen ya kai ga kama ɗimbin waɗanda ake zargi da wannan laifi tare da kwato kayayyakin shaida daban-daban, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Sai dai ya ce an tsinci da dama daga cikin waɗanda aka tsare a mace da sanyin safiyar 17 ga Satumba, bayan abin da ya bayyana a matsayin barkewar wata cuta da ake zargi.
NSCDC ta tabbatar da mutuwar
Sanarwar NSCDC ta ce:
“Hukumar Tsaron ta NSCDC ta Neja, a wani yunƙurinta na kawar da ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a jihar, ta gudanar da wani samame a ranakun 15 da 16 ga Satumba 2026."
“Samamen ya haifar da gagarumin sakamako, inda aka kama ɗimbin waɗanda ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba tare da kwato kayayyakin shaida daban-daban.
“Duk da haka, da sanyin safiyar 17 ga Satumba 2026, an taras da waɗanda aka tsare a mace sakamakon barkewar wata cuta da ake zargi."

Source: Original
Har zuwa lokacin da aka haɗa wannan rahoto, ba a bayyana musabbabin mutuwar mutanen da kuma irin cutar da ake zargin ta barke ba.
Mutane sun farmaki ofishin NSCDC
Kun ji cewa wasu fusatattun mutane sun cinna wa ofishin hukumar NSCDC wuta a Kano tare da kashe mutane uku da ake zargi da satar babura.
Mutanen sun buƙaci jami'an da su miƙa musu waɗanda ake zargin domin su kashe su da kansu, lamarin da ya jawo rigima ta barke a cikin ofishin.
Asali: Legit.ng
