Wata Matashiya mai ‘Ya ‘ya 3 ta mikawa Gwamnati kokon bararta
Wata Matashiyar Mahaifiya mai suna Khafila Bashiru mai zama tare da ‘Ya ‘yan ta a cikin wata Unguwa da ke cikin juji a jihar Katsina ta kai kukanta gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Legit.ng ta yi arba da wannan Baiwar Allah mai ‘Ya ‘ya uku wanda ta ke neman taimako. Khafila Bashiru ta nemi gwamnatin Najeriya ta duba lamarinsu, ta kawo masu doki na halin da su ke ciki.
Bashiru mai shekaru 29 a Duniya ta bayyanawa Legit.ng cewa a wannan bola su ke zama da ita da sauran Makwabtan ta, kuma ba su da niyyar a canza masu matsuguni amma su na neman agaji.
Uwar ‘Ya ‘ya ukun ta yi kira ga ‘yan jarida su yi amfani da muryarsu wajen ganin gwamnati ta sama masu aikin yi. Matar ta ce za su iya yin duk aikin da aka ba su domin su samu na kashewa.
KU KARANTA: Sojoji na zargin Gwamnoni da lamuke kudin Talakawa da sunan tsaro
Khafila Bashiru ta nuna cewa hankalinsu kwance su ke zama a cikin shara da datti, sai dai abin da su ke kiran gwamnati ta yi masu shi ne ta sama masu aikin da zai zama hanyar cin abincinsu.
Wannan Mata da har yanzu ta ke da sauran kuruciya, ta ce su kan yi kalar tarkace ne kamar takardu, ledoji da gwangwani, su kai kamfani. A haka ne ake ba su kudin batarwa idan an juya su.
A hirar ta da Legit.ng ta yi kokarin yin Ingilishi amma dole ta rika gaurayawa da Yarbanci, ta ce wahala ta sa ta zama mummuna saboda sai sun yi da gaske su ke iya samun N50 a duk rana.
A yayin da wannan Mata ta ke magana, akwai jariri goye a bayanta. Sai dai ta na ganin cewa bai kamata Diyar da ta haifa, ta tashi ta samu kanta a cikin irin wannan hali na rayuwar kaskanci ba.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng